Ummi Nuhu: Tsohuwar 'Yar Fim Ta Rusa Kuka a Idon Duniya, Ta Fadi Halin da Ta Shiga

Ummi Nuhu: Tsohuwar 'Yar Fim Ta Rusa Kuka a Idon Duniya, Ta Fadi Halin da Ta Shiga

  • Tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Nuhu, ta bayyana yadda rashin karɓuwa ya hana ta komawa harkar fim
  • Ummi Nuhu ta ce ta taba burin kawowa Kannywood, amma sau da dama tana jin kamar an manta da ita gaba ɗaya
  • Yayin da ta yi bayani kan aure da wasu abubuwa, tsohuwar jarumar ta ce fim ne abin da ta fi iyawa a rayuwarta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu, ta bayyana damuwarta cikin kuka yayin wata hira da aka yi da ita.

A yayin hirar, Ummi Nuhu ta bayyana yadda gaza komawa harkar fim ya ci mata tuwo a ƙwarya har ta hakura.

Ummi Nuhu ta rusa kuka ana tsaka da hira da ita.
Ummi Nuhu ta rusa kuka ana tsaka da hira da ita. Hoto: Gabon TV
Source: Youtube

A hirar da ta yi da Gabon TV, Ummi Nuhu ta bayyana cewa duk da tana da kwarewa da gogewa a harkar fim, zamaninta ya wuce ba tare da ta samu damar dawowa ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kotu ta daure fitaccen mawaki Hamisu Breaker wata 5 a gidan yari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin Ummi Nuhu da shigarta Kannywood

Ummi ta ce an haife ta a Kaduna duk da cewa asalin iyayenta 'yan Bunkure ne a Jihar Kano, kuma a Kaduna ta yi makaranta, ta shiga Kannywood.

Ta bayyana cewa fim dinta na farko shi ne 'Al’amari' na Ibrahim Babangida, inda ta yi zamani da fitattun jarumai irin su Fati Baffa da Masura Isah.

Ummi Nuhu ta rusa kuka ana tsakar hira

Cikin hawaye Ummi Nuhu ta bayyana cewa ta yi ƙoƙarin dawowa masana’antar amma tana jin kamar an cire ta daga jerin waɗanda ake bukata.

Cikin kuka da nuna damuwa ta ce:

“Akwai lokacin da za ki ga kamar an daina yi da kai. Da na yi, na yi kawai sai na hakura.”

Tsohuwar jarumar ta bayyana cewa ba ta da lafiya sosai a yanzu, kuma hakan na daga cikin dalilan da suka hana ta komawa sana’ar fim.

Kara karanta wannan

'Kwankwaso na tsaka mai wuya a siyasa tsakanin shiga APC, PDP ko ADC,'

Shawarar Ummi Nuhu ga matasa da batun aure

Ummi ta shawarci masu tasowa da su cire hassada da kin juna a rayuwarsu, domin rayuwa tana iya juya wa mutum.

Kan batun aure kuwa, tsohuwar jarumar ta bayyana cewa har yanzu ba ta taba yin aure ba a rayuwarta.

Hadiza Gabon da ke shirya hira a Gabon TV
Hadiza Gabon da ke shirya hira a Gabon TV. Hoto: Hadiza Gabon
Source: Instagram

Batun hadarin mota da soyayyar jama'a

Ta tuna da wani lokaci da ta yi hadari har aka saka sojoji su ba da tsaro saboda yawan jama’ar da suka zo gaishe ta.

A karshe, Ummi Nuhu ta ce Ali Nuhu ne mutum ɗaya da ba za ta taɓa mantawa da shi ba saboda taimakon da ya mata sau da dama.

Ta ce a baya-bayan nan ma tana cikin wani hali da mutane da dama suka ki taimaka mata, sai da ta kira Ali Nuhu ya ceto ta.

Legit ta tattauna da malamin addini

Wani malamin Musulunci a jihar Gombe, Ustaz Musa Yahaya ya yi kira ga matasa musamman mata da su yi hankali da rayuwa.

Kara karanta wannan

Tsohuwar matar kwamishina ta kwance masa zani a kasuwa, ta roki gwamna Bago alfarma

A cewar shi:

"Ba sai 'yan fim ba ne kawai za su dauki darasi a kan labarinta, duk wanda ya ke yin wani abu maras kyau ya kamata ya dauki darasi.
"Matasa, musamman mata su kara hankalta, su guji aikata abin da zai jawo musu da-na-sani."

Malami ya yi wa Adam Zango jaje

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan shari'a a lokacin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana kan hadarin da Adam A Zango ya yi.

Abubakar Malami ya bayyana cewa a lokacin da Adam Zango ya yi hadari baya Najeriya, amma ya sanya shi a addu'a.

Legit Hausa ta rahoto cewa tsohon ministan ya roki Allah ya ba jarumin lafiya tare da kiyaye shi daga irin haka a nan gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng