Zargin Satar Fasaha: Ali Jita Ya Gamu da Babbar Matsala bayan Sakin Sabuwar Waka

Zargin Satar Fasaha: Ali Jita Ya Gamu da Babbar Matsala bayan Sakin Sabuwar Waka

  • Ana zargin mawaki Ali Jita da satar baitocin wakar Amarya daga wani babban dan jarida Yakubu Musa, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce
  • Hassan Yakubu ya bai wa Ali Jita wa’adin awanni 72 ya bada hakuri ko ya fuskanci ƙara bisa zargin satar fasaha daga wakar Yakubu
  • Bincike ya nuna cewa baitocin wakar Ali Jita na Amarya sun yi kama da na Yakubu Musa da aka wallafa kwanaki 21 kafin wakar Jita

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Ana zargin fitaccen mawakin Kannywood, Ali Jita ya saci fasaha a sabuwar wakar da ya fitar mai taken 'Shalelen miji (Amarya)'.

Ali Jita ya fitar da wannan waka ta Amarya a matsayin martani ga wakar 'Uwar Gida' da ya fitar a kwanan baya, wacce ta jawo ce-ce-ku-ce.

Ana zargin Ali Jita ya saci fasahar wani mawaki Yakubu Musa a sabuwar wakarsa ta Amarya
Ali Jita ya nishadantar da jama'a a wani taron baje kolin kamfanin taliyar Crown. Hoto: Ali Jita
Source: Facebook

Ana zargin Ali Jita ya saci fasaha

Kara karanta wannan

'Ya taɓa korarmu kan N15': Diyar Buhari game da tarbiyya da mahaifinsu ya ba su

Wani ma'abocin Facebook, Hassan Yakubu, ya wallafa a shafinsa cewa suna zargin mawakin ya saci baitocin da ya yi wakar Amarya da su daga wani Yakubu Musa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hassan Yakubu ya wallafa cewa:

"Mun ba Ali Jita wa'adin awanni 72 ya ba da hakuri.
"Ku biyo ni!
"Magana ta gaskiya, duk da ni ba Lauya bane, wannan babbar magana ce.
"In har Ali Jita ba zai iya gabatar da hujjoji da za su nuna cewa ya riga matashin mawakin Arewa, mai mugu mugun tashe, watau, Yakubu Musa yin wannan wakar ba, kuma bai tuntubi matashin mawakin ba kafin ya nadi sautin wakar ba, Yasin, ofishin Dino Melaye ya samu karar farko da zai fara zuwa kotu.
"Za mu yi aiki tare da Shettima da Umar Sani Bebeji kamar yadda nayi magana a baya. Wannan magana ce ta zargin satar fasaha."

Baitukan da ake zargin Ali Jita ya sata

Duk da dai wannan bawan Allah ya yi maganar cikin raha ne, sai dai Legit Hausa ta fahimci Yakubu Musa ya fara yin baitocin tun a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Buhari, an hango babban kuskuren da Shugaba Tinubu ya yi

A tare da wannan sako da Hassan Yakubu ya wallafa, akwai hoton shafin Yakubu Musa na Facebook, wanda ya nuna cewa Yakubu ya rubuta baitin wakar Amarya a ranar 26 ga Yunin 2025.

Baitukan da Yakubu Musa ya rubuta su ne:

"Amarya mai Dignity
"Kin kawo mana Unity
"Auran kore Poverty
"Kin kwace Authority
"Kin dakile Impunity
"Kin ba megida Neutrality
"Ba zancan Majority"

Ya ci gaba da cewa:

"Sannu amarsun Integrity
"Kin shigo da Velocity
"Komai naki da Density
"Soyyaya mai Intensity
"Ga shagwabar Subtlety
"Komai tsaf Simplicity
"Allah kawo Fertility
"Gida 2 kwai Tranquility"

Kalli bidiyon wakar Jita a nan kasa:

Ana zargin Ali Jita ya saci fasaha a sabuwar wakar 'Amarya' da ya fitar
Ali Jita ya nishadantar da jama'a a wani taron baje kolin kamfanin taliyar Crown. Hoto: Ali Jita
Source: Facebook

Ali Jita ya saci baitocin Yakubu Musa?

Legit Hausa ta fahimci cewa Ali Jita ya wallafa bidiyon wakarsa ta 'Amarya' a shafinsa na YouTube a ranar 13 ga watan Yulin 2025, kusan kwanaki 21 da bayyanar wakar Yakubu Musa.

A cikin wakarsa, Ali Jita ya yi amfani da wadannan baitocin daga mintuna na 1:30 zuwa 2:00. Sai dai kuma, ba duka yadda Yakubu Musa ya jero baitocinshi Ali Jita ya rera ba.

Mawaki Ali Jita ya yi amfani da wasu daga cikin zubin baitocin Yakubu Musa a wakokinsa, yayin da ya canja wasu, amma duk abu daya suke nufi, a inda ya yi amfani da kafiyar 'ti'.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da bayyana ayyukan alheran Buhari, Malami faɗI abin da ya sani

Ali Jita ya fice daga NNPP, ya koma APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mawaki Ali Isah Jita ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya ya koma APC ta hannun Sanata Barau Jibrin.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau wanda ya tubewa Ali Jita jar hula ya ce yana farin ciki da mawakin ya koma jam'iyyar mai ci.

A cewar Sanata Barau, Ali Jita ya daukarwa APC alkawarin cewa a shirye yake ya yi aiki tukuru domin ganin jam'iyyar APC ta samu nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com