Ba a daukar mawaka da 'yan fim da muhimmanci a arewa - Ali Jita

Ba a daukar mawaka da 'yan fim da muhimmanci a arewa - Ali Jita

Sanannen mawakin Hausa, Ali Isa Jita ya ce Arewacin Najeriya ba a daukar mutane irinsu da muhimmanci. Ana daukar mawaka da 'yan fim a mutanen banza ne.

Ali Jita ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da shafin Hausa na BBC Instagram inda ya ke cewa "ana yi mana wani kallo ne na mutanen da basu da makoma."

Ya kara da cewa "yanzu za ka ga mawakan sun fara yin wake da Turanci domin janye hankalin wadanda basu jin Hausa.

"Wasu hausawan wai ba sa son su saurare mu har suna nuna ba sa jin Hausar."

Dangane kuma da wakokinsa, Jita ya ce kawo yanzu, bai san adadin wakokin da yayi ba amma dai kundin wakoki ya fita da kamar 10.

Koda aka tambayeshi inda ya samo lakabin Jita, mawakin yace "tun ina yaro ne nake yawo da jita har zuwa lokacin da na fara shiga studio domin waka.

"A lokacin da na fara shiga studio, sai nace a yi min kida da jita domin ita na fi so a wannan lokacin. A take kuwa Adam Zango ya sa mun suna Ali Jita."

Ba a daukar mawaka da 'yan fim da muhimmanci a arewa - Ali Jita
Ba a daukar mawaka da 'yan fim da muhimmanci a arewa - Ali Jita. Hoto daga Soundcloud
Source: Getty Images

KU KARANTA: COVID-19: Ba mu yi fushi ba, za mu sake tura tawagar kwararru Kogi - FG

Game da wacce wakar ce bakandamiyarsa, Jita yace bashi da bakandamiya illa iyaka yace duk wakar da ta shiga kasuwa sosai ta kan zama bakandamiyarsa.

Jita ya bayyana cewa, ya fara waka ne tun yana makarantar Islamiyya inda ya zama jagaban masu wake a makarantar.

Da aka tambayi mawakin sana'arsa banda waka, ya ce in dai waka ta kare to fawa zai koma don kuwa mahaifinsa sana'arsa kenan.

A wani labari na daban, A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a sake tura tawagar kwararru jihar Kogi don tabbatar da cewa an samar da abubuwan da jihar ke bukata wajen yaki da cutar coronavirus.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bada wannan sanarwan a Abuja ga taron manema labarai yayin da suke tattaunawa da kwamitin yaki da cutar coronavirus na fadar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel