'Shiga Fim ne Ya Hana ni Zama Malamin Musulunci': Jarumin Kannywood Ya Fadi Gaskiya
- Fitaccen jarumin Kannywood, Abubakar Waziri ya ce da ba ya harkar fim, da ya zama malamin addini saboda yana da sha’awar gyaran al’umma da wa’azi
- Jarumin da aka fi sani da Baba Rabe ya bukaci malamai su shiga harkar fim domin yawancin jama’a yanzu suna kallon fim fiye da sauraron wa’azi
- Ya ce mutane suna yi wa jaruman fim kudin goro, duk da cewa ba dukansu ke da matsaloli ba, ya ce ya kamata a fahimce su
- Baba Rabe ya bukaci a hada kai wajen tsaftace Kannywood domin tsaftace masana'antar da ake korafi kanta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jarumin Kannywood, Abubakar Waziri ya ce akwai bukatar malamai su shiga harkar fim domin gyara.
Jarumin da aka fi sani da Baba Rabe ya ce a yanzu mutane sun fi kallon fina-finai fiye da sauraron wa’azi, don haka ya kamata a hada kai wajen gyaran Kannywood.

Kara karanta wannan
'Babu dole a addini': Gwamna ya hana wa'azi a bainar jama'a, ya fadi tarar da za a biya

Asali: Facebook
Gudunmawar Baba Rabe a Kannywood
Baba Rabe ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da DW Hausa ta yi hira da shi da aka wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jarumin ya ce shi dan asalin Zaria ne, ya karanci Al’adun Gargajiya a ABU Zaria, sannan yana aiki da Abuja 'Council For Art And Culture'.
Waziri ya bayyana cewa ya fara aiki a ABU Zaria a matsayin dan wasan kwaikwayo kafin ya shiga harkar fim da nishadantarwa.
Ya kara da cewa kafin fim, ya wakilci Najeriya a kasashe da dama kamar Amurka, China, Korea da sauransu a fannin wasan kwaikwayo.
Ya ce yanzu kuwa yana cikin masana'antar Kannywood a matsayin jarumi, yana amfani da wannan dama wajen tallata al’adu da kuma ilmantar da jama’a.

Asali: Facebook
Yadda Baba Rabe ya shawarci malaman Musulunci
A kan yadda ake ganin jaruman fim a matsayin masu girman kai, ya ce wannan zargi ba gaskiya ba ne ko kadan.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Yaran Bello Turji sun sace ɗan Isiyaka Rabiu, matashin ya yi roko a bidiyo
Ya bayyana cewa kasancewarsu ‘sannanu a idon al'umma’ na janyo mutane su rika neman ko daukar hoto da su ko da ba su shirya hakan ba.
Saboda haka wani lokaci sukan kasa aiwatar da abinda suka fito domin yi, saboda yawan bukatu da daukar hankali.
Ya ce mutane su daina hukunta duka jarumai saboda kuskuren mutum daya, domin kowa da dabi’arsa daban.
A karshe, ya bukaci malamai su shiga harkar fim su taimaka wajen gyaranta ba wai su ci gaba da suka daga gefe ba.
Ya ce:
“Da a ce ni ba dan fim ba ne, da tabbas zan zama malamin addinin Musulunci saboda ina matukar sha’awar gyaran al’umma.”
Jarumar Kannywood ta shiga kotu da mijinta
A baya, Legit Hausa ta ruwaito muku cewa Jaruma Maryam Malika, ta kai kara kotun Shari’a inda ta bukaci a tabbatar da sakin da tsohon mijinta ya yi mata shekarun baya.
Lauyanta ya bayyana cewa tsohon mijin nata ya yi mata saki na uku shekaru biyar da suka wuce bayan ta nemi saki ta hanyar Khul’i.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng