Jamilun Jidda da Wasu Sababbin Finafinan Kannywood 5 da Za a Fara Haskawa a 2025
Kano - Masu shirya finafinai a masana'antar Kannywood sun wasa wukakensu yayin da suka shirya fitar da sababbin finafinan da suka dauka a shekarar 2024.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Shekarar ta 2025 za ta zamo shekarar da za a ga sababbin finafinan Hausa da salon daukarsu ya sha bamban da na baya, kama daga hoto, zubin labari da kuma jarumai.
Finafinan Kannywood 6 da za a haska a 2025
Tun a karshen shekarar 2024, Legit Hausa ta fahimci cewa masu shirya finafinan Hausa na sanarwar fara haska wasu sababbin finafinansu a shekarar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan masu shirya finafinan Hausa da suka hada da Abubakar Bashir Maishadda, Falalu A Dorayi, Shareef Studios, Nazir Dan Hajiya da sauransu, suna dauke da sababbin finafinai a wannan shekarar.
Mun zakulo maku wasu sababbin finafinan da ake sa ran za a fara haska su a 2025:
1. 'Gidan Badamasi' - Falalu A. Dorayi
Shirin farko da masu kallo suka dade suna tsumayin dawowarsa shi ne shiri mai dogon zango na 'Gidan Badamasi' daga kamfanin Dorayi Film Production.
Duk da cewa fim din Gidan Badamasi ba sabo ba ne, amma dai mutane na tsumayin fara ganin Zango na shida na shirin, wanda tuni aka fara kallonsa a Arewa on Demand.
A 'yan kwanaki masu zuwa ne ake sa ran gidan talabijin na Arewa24 za su fara haska shi a talabijin yayin da suka fara haska shi a manhajarsu ta Arewaondemand.
Wanda ya shirya shirin, Falalu A Dorayi ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa shirin gidan Badamasi zango na shida zai zo da sabon salon barkwanci da ba a taba gani ba.
Kalli tallar shirin a nan kasa:
2. 'Jamilun Jidda' - Abubakar Bashir Mai Shadda
Fim din Jamilun Jidda sabon fim ne fil a leda, daga kamfanin fitaccen mai shirya finafinai Abubakar Bashir Mai Shadda.
Tun a shekarar 2024 Abubakar Bashir Maishadda yake sanarwa a shafinsa na Instagram cewa za a fara haska fim din Jamilun Jidda daga ranar Asabar, 11 ga watan Janairu, 2025.
Za a rika kallon shirin a tashar Arewa24 da misalin karfe 9:00, inda za a ga jarumai da suka hada da Sadiq Sani Sadiq, Ali Nuhu, Nura Hussain, Firdausi Yahaya, Fatima Hussain da sauransu.
A sanarwar da Maishadda ya yi a shafinsa na Instagram ya ce Jamilun Jidda dauke da sakon addinin Musulunci, soyayya tsakanin mata da miji, kishi, tausayi da kuma ban al’ajabi.
Kalli tallar shirin a nan kasa:
3. 'Da Za Ki So Ni' - Umar M Shareef
Shiri na uku da ake tsumayin fara kallonsa a shekarar 2025 shi ne shirin kamfanin Shareef Studios mai suna 'Da Za Ki So Ni.'
Shirin Da Za Ki So Ni shir ne da ya samu shiryawa daga Umar M Shareef sannan Mustapha M Shareef ya ba da umarni.
A zantawarmu da jarumi Abdul M Shareef, wanda ya dauki nauyin shirin, ya ce labarin 'Da Za Ki So Ni' zai kasance mafi soyuwa ga masu kallon da ke son labaran soyayya.
"Shirin zai sanya mai kallo ya zubar da hawaye saboda tausayi, sannan zai nuna karfin sadaukarwar soyayya da kuma yadda soyayya ke iya zautar da mai hankali.
"Mai kallo ba zai yi da na sanin kallon shirin Da Za Ki So Ni ba domin yana dauke da manyan jarumai, kamar Ali Nuhu, Maryam Malika, Zahra Diamond da ni kai na."
- A cewar Abdul M. Shareef.
Har zuwa yanzu dai ba a sanya ranar da za a fara haska wannan shirin na Da Za Ki So Ni ba, amma Abdul M Shareef ya ce a yi dakon kallonsa a wannan shekarar ta 2025.
Kalli tallar shirin a kasa:
4. Matar Mijinta - Sadiq N Mafia
A shekarar 2025, masu kallo za su kayatu da kallon shirin 'Matar Mijinta' mai dogon zango, wanda fitaccen mai ba da umarni, Sadiq N Mafia ya shirya da kansa.
Shirin 'Matar Mijina' na dauke da fitattun jarumai da dama da suka hada da Yakubu Muhammad, Lawan Ahmad, Aisha Izzar So, Khadija Muhammad, Umar Gombe da sauransu.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Sadi N. Mafia ya sanar da cewa sun saki tallar shirin 'Matar Mijina' a ranar 1 ga watan Janairun 2025.
Sai dai Legit Hausa ta duba, ba ta samu wannan tallar ba, amma dai an tabbatar da cewa shirin zai kayatar da masu kallo musamman ganin ya shafi rigimar aure.
5. Al'ummata - Sani Candy
Daya daga cikin finafinan da ake fatan za su taka muhimmiyar rawa a Kannywood a 2025 shi ne 'Al'ummata.' Shiri ne mai dogon zango daga kamfanin S.Y.C Multimedia LTD.
Fitacciyar jaruma, Hadiza Gabon ce ta kawo wannan labarin wanda ya samu shiryawa daga Sani Candy yayin da Ali Gumzak da MS Elgasash suka ba da umarni.
Shirin Al'ummata, ya samu fitowar manyan jarumai da suka hada da, Rabiu Rikadawa, Alasan Kwalle, Jamila Umar, Falalu A Dorayi, Baballe Hayatu, Asma'u Sani da sauransu.
Ana kyautata zaton cewa duk shirin da aka hada jarumai irin wannan, zai kayatar da masu kallo saboda kowannensu ya kware kuma yana da baiwar nishadantar da masu kallo.
A wannan shekarar ta 2024 ake sa ran fara kallon wannan kayataccen shiri na Al'ummata.
6. 'Miji Na' - Nazir Danhajiya
Har ila yau, masu kallo za su fara kallon shirin 'Miji Na' mai dogon zango daga ranar 9 ga wata Janairun 2025 a shafin Youtube na Dan Hajiya Films Production.
Babban mai shirya fina-finai, Nazir Danhajiya ne ya shirya wannan shirri wanda ke dauke da fitattun jarumai irinsu Shamsu Dan Iya, Momee Gombe, Baballe Hayatu da sauransu.
Mai shirya shirin, ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa za a rika haska fim din da misalin karfe 8:30 na kowacce ranar Alhamis.
Kasancewar Nazir Danhajiya ya saba kawo finafinan da suke da kayatarwa, ana sa ran shi ma wannan sabon shirin zai nishadantar da masu kallo a 2025.
Finafinan Kannywood da suka yi tashe a 2024
A wani labarin, mun ruwaito cewa masu shirya finafinan Hausa sun yi matukar kokari wajen samar da finafinai masu dogon zango da suka kayatar a shekarar 2024.
Legit Hausa ta zakulo wasu fitattun finafinan Kannywood da suka yi tashe a shekarar da ta gabata ciki har da Manyan Mata, Labarina da dai sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng