Jerin 'Yan Kannywood 8 da Suka Rabauta da Mukami a Gwamnati bayan Zaben 2023

Jerin 'Yan Kannywood 8 da Suka Rabauta da Mukami a Gwamnati bayan Zaben 2023

Ƴan Kannywood da dama sun taka rawar gani a lokacin da ake buga kambun siyasar zaɓen 2023 a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jaruman masana'antar da dama sun tallata ƴan takara daga jam'iyyun siyasa daban-daban a lokacin zaɓen.

Jaruman Kannywood da suka samu mukamai
Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun samu mukamai a gwamnati Hoto: @alinuhu, @abbaelmustaph1, @Rahama_sadau
Asali: Twitter

Ƴan Kannywood sun samu muƙamai

Wannan ƙoƙarin da suka yi ya sanya wasu daga cikinsu sun rabauta da muƙamai a gwamnatocin tarayya da jihohi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga wasu daga cikin ƴan masana'antar Kannywood da suka samu muƙaman gwamnati a matakai daban-daban.

1. Ali Nuhu

Ali Nuhu ya samu muƙamin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun kai wani harin ta'addanci

Tuni fitaccen jarumin, furodusa kuma darakta ya fara aiki a hukumar wacce take a ƙarƙashin ma'aikatar al'adu.

Naɗin na sa dai ya jawo murna sosai daga wajen ƴan Kannywood inda suke kallon hakan a matsayin babbar nasara a gare su.

2. Abba El-Mustapha

Abba El-Mutapha ya samu muƙamin shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

Jarumin na Kannywood ya samu muƙamin a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Abba El-Mustapha ya kasance na gaba-gaba wajen tallata gwamnan a lokacin yaƙin neman zaɓe.

3. Sunusi Oscar 442

Sunusi Hafiz wanda aka fi sani da Sanusi Oscar 442 ya rabauta da muƙami a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.

Fitaccen daraktan a Kannywood, ya samu muƙamin mai ba Gwamna Abba shawara na musamman a kan harkokin Kannywood.

4. Rahama Sadau

Rahama Sadau na ɗaya daga cikin ƴan Kannywood da ake damawa da su a gwamnati bayan sun samu muƙami.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rantsar da zababbun ciyamomin APC, ya ja musu kunne

Jarumar ta samu shiga cikin kwamitin bunƙasa zuba jari ta hanyar amfani da fasahar zamani watau iDICE.

Kwamitin na iDICE yana a ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Jarumar ta nuna godiyarta ga shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima a shafinta na X bayan an sanar da naɗin a watan Afrilu.

5. Bashir Lawandi Datti

Bashir Lawandi Datti ya samu muƙamin kwamishina a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau.

Jarumin kuma furodusa a masana'antar Kannywood ya samu muƙamin kwamishinan matasa da wasanni inda daga bisani aka sauya shi zuwa kwamishinan albarkatun ruwa da makamashi.

Bashir Lawandi Datti ya yi takarar kujerar majalisar dokokin jihar Plateau sau biyu a shekarar 2019 da 2024, amma bai samu nasara.

6. Tijanni Gandu

Tijjani Hussaini Gandu ya samu muƙamin mai ba gwamnan Kano shawara na musamman kan harkokin mawallafa.

Fitaccen mawaƙin na siyasa ya yi suna wajen rera waƙoƙi ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa Tinubu ya fadi lokacin da 'yan Najeriya za su gode masa

7. Rabiatu Sulaiman Kurfi

Rabiatu Sulaiman Kurfi ta samu muƙamin mai ba gwamnan Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda, shawara a kan kafofin sadarwa na zamani.

Jarumar ta taka rawa a shirin Kwana Casai'in mai dogon zango na tashar Arewa 24.

8. Maryam Abubakar 'Jankunne'

Maryam Abubakar Jankunne ta samu muƙamin babbar mai ba gwamnan Kano shawara kan matan karkara.

Tauraruwar ta shahara sosai bayan ta fito a wani fim da aka sa wa suna Jan kunne

Jarumar Kannywood ta ba mata shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu da aka fi sani da Hadiza Gabon ta yi maganar 'yan mata masu shirin shiga fim.

Hadiza Gabon ta ce akwai abubuwan da ya kamata yan mata su maida hankali a kai domin gina rayuwa mai kyau maimakon shiga fim, zancen ya jawo surut.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng