“Za Mu Taimake Shi”: Ali Jita Ya Magantu Kan Halin da Adam a Zango Yake Ciki

“Za Mu Taimake Shi”: Ali Jita Ya Magantu Kan Halin da Adam a Zango Yake Ciki

  • Fitaccen mawaki, kuma mai shirya fina-finan Hausa, Ali Jita, ya yi magana kan halin kuncin rayuwa da jarumi Adam A Zango yake ciki
  • Ali Jita ya ce Adamu mutumin kirki ne kuma lokaci ya yi da ya kamata 'yan fim da mawaka duk su fito su ja shi a jika tare da neman mafita
  • Idan ba a manta ba, mawaki Zango ya saki wani bidiyo wanda yake nuna irin butulcin da ya ce wasu 'yan Kannywood sun yi masa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fitaccen mawaki, kuma mai shirya fina-finan Hausa, Ali Jita, ya yi magana kan halin kuncin rayuwa da jarumi Adam A Zango yake ciki.

Kara karanta wannan

"Ban son zama ubangida" Malam El-Rufa'i ya mayar da martani kan abin da ke faruwa a Kaduna

Ali Jita ya yi magana kan halin da Adam A Zango yake ciki
Ali Jita ya tabbatarwa da duniya cewa Adam A Zango mutumin kirki ne. Hoto: @princeazango, @alijitaa
Asali: Twitter

Ali Jita wanda ya yi martani kan bidiyon Zango a shafinsa na TikTok a ranar safiyar ranar Litinin, ya ce lokaci ya yi da ya kamata 'yan Kannywood su taimaki Adam A Zango.

"Daukaka ba alkairi ba ce" Adam A Zango

Mawaki Zango ya dauki wani faifan bidiyo wanda ya fadawa duniya irin jarabawar rayuwar da yake fuskanta, kamar yadda shafin Arewa Focus ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na ba mutane da dama gudunmawa a Kannywood, amma basu taba yabo na ba sai dai su yabi wani daban saboda ni wulakantacce ne a wajensu.
"Daukaka ba alkairi bace, kullum kana nunawa duniya kana da kudi kuma ba ka da matsala, amma a zahirance kafi kowa fuskantar kalubale, kuma babu hali ka fito ka fada."

Wadanda Adam Zango ya taimaka a Kannywood

Kara karanta wannan

Adam A Zango ya fitar da sabon faifan bidiyo kan halin da ya ke ciki, ya yi godiya

Adam Zango ya lissafa wadanda ya ba kyautar mota a masana'antar da suka hada da Falalu A Dorayi, Sadiq N. Mafia, Tahir I. Tahir, Abubakar Sani, Kabiru, Rabiu, Umar Big Show.

Wadanda ya taimaka suka samu daukaka a Kannywood kamar yadda ya zayyana, sun hada da:

"Fati Nijar, Nazifi Asnanic, Zainab Raga, Zainab Indomie, Ali Jita, Isah Feruskan, Umar Big Show, Ado Gwanja, Ussaini Danko, Umar M. Shareef da Sadiq Sani Sadiq."

"Adamu mutumin kirki ne" - Ali Jita

A wannan gabar ne, mawaki Ali Jita ya yi martani kan kalaman na Zango, inda ya gasgata dukkanin abin da ya fada tare da cewa:

"Adamu mutumin kirki ne kuma zuciyarshi tana da kyau, ba shakka ya taimake ni da sauran wadanda ya lissafa. Ina amfani da wannan dama in bashi hakuri a madadinmu gaba daya.
"Ina ganin yanzu lokaci ya yi da ya kamata 'yan fim da mawaka duk mu fito mu ja Adamu a jiki, mu gane matsalolin da aka samu a baya domin a gyara su."

Kara karanta wannan

Ali Nuhu ya fito ya gayawa duniya halin da Adam A. Zango ya samu kansa a ciki

Ali Jita ya yi nuni da cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba, don haka za su zauna da Zango a kungiyance domin yi wa dukkanin tufkar hanci.

"Adamu na cikin koshin lafiya" - Ali Nuhu

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa jarumi Ali Nuhu ya fitar da sanarwa a shafinsa na Facebook da ta nuna cewa jarumi Adam A Zango na nan cikin koshin lafiya.

Ali Nuhu ya yi wannan sanarwar ne biyo bayan rubututtuka da bidiyo da mawaki Zango ya wallafa a soshiyal midiya wanda yake nuna irin mawuyacin halin da yake ciki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.