Kotu Ta Haramtawa Hukumar Tace Fina Finai Ta Kano Dakatar da Kamfanoni 3 na Kannywood

Kotu Ta Haramtawa Hukumar Tace Fina Finai Ta Kano Dakatar da Kamfanoni 3 na Kannywood

  • Wata babbar kotu da ke zamanta a birnin Kano ta warware dakatarwar da aka yi wa wasu kamfanonin Kannywood guda uku
  • Kotun ta haramtawa hukumar tace fina-finata ta jihar daga dakatarwa ko yin katsalanan a ayyukan kamfanonin
  • An ɗauki wannan matakin ne bayan kamfanonin sun kai ƙarar hukumar da shugabanta a gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata babbar kotun jihar Kano ta amince da buƙatar wasu kamfanonin Kannywood kan hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da shugabanta Abba El-Mustapha.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Hadiza Suleiman ta amince da hakan ne a ranar Juma’a, 12 ga watan Afirilun 2024, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kotu ta hana dakatar da kamfanonin Kannywood
Kotu ta warware dakatarwar da hukumar tace fina-finan ta yi wa kamfanonin uku Hoto: Abba El-Mustapha 1
Asali: Facebook

Kotun ta haramtawa hukumar dakatarwa ko yin katsalandan ga ayyukan kamfanonin guda uku na masana’antar Kannywood.

Kara karanta wannan

Gwamna mai-ci ya ce shugabannin da ke goyon bayan tsohon gwamna sun shiga uku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta kuma bada umurnin hana ma'aikata, wakilai, ko duk wani wanda ke wakiltar su dakatarwa ko tsoma baki a ayyukan waɗannan kamfanoni guda uku.

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Kannywood Enterprises LTD, Amart Entertainment, da Hajiya A’isha Tijjani, yayin da waɗanda ake ƙarar su ne hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da Abba El-Mustapha.

Wane hukunci kotun ta yi?

Bugu da ƙari, kotun ta amince da buƙatar da masu shigar da ƙara suka gabatar ta hannun lauyansu, Barista AA Rabi’u Doka, ta yin watsi da duk wani hukunci, umurni da waɗanda ake ƙara suka bayar a kansu a ranar 15 ga Fabrairun 2024.

Kotun ta kuma amince da buƙatar masu shigar da ƙarar ta su ci gaba da gudanar da harkokinsu na halal har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron ƙarar da ke gabanta.

Kara karanta wannan

Karamar Sallah 2024: Gwamnatin Kano ta tallafawa mazauna gidan gyaran hali da abinci da shanu

Daga nan sai mai shari’a Hadiza Suleiman ta ɗage ƙarar zuwa ranar 29 ga Afrilu, 2024, domin fara zaman shari'a.

An dakatar da jarumi a Kannywood

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta laftawa Abdul Saheer haramcin duk abin da ya shafi harkar fim har na shekaru biyu.

Ana dai zargin jarumin wanda aka fi sani da Malam Ali a shirin Kwana Casain da wallafa bidiyo mai dauke da batsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng