Karamar Sallah 2024: Gwamnatin Kano ta Tallafawa Mazauna Gidan Gyaran Hali da Abinci da Shanu

Karamar Sallah 2024: Gwamnatin Kano ta Tallafawa Mazauna Gidan Gyaran Hali da Abinci da Shanu

  • Gwamnatin jihar Kano ta kai kayan abinci gidan gyarin hali dake jihar domin bawa daurarru damar yin shagulgulan sallah karama cikin walwala
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayar da kayan ta hannun shugabar kwamitin nemawa daurarru afuwa, Azumi Namadi Bebeji
  • Ana gudanar da bukukuwan sallah karama daga yau Laraba bayan kammala azumin watan Ramadana na kwanaki 30 a jiya Talata

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Gwamnatin jihar Kano ta raba kayan abinci da shanu ga waɗanda ke gidan gyaran hali a jihar domin su warwasa da sallah ƙarama.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa kayan abincin ne ta hannun shugabar kwamitin nemawa ɗaurarru afuwa a jihar, Azumi Namadi Bebeji.

Kara karanta wannan

Goron Sallah: Gwamnan Bauchi ya faranta ran ma'aikatan jihar

Abba Yusuf ya bayar da abinci ga gidan gyaran hali a jihar Kano
Gwamnatin ta raba kayan ne domin daurarru su yi shagulgulan sallah cikin nishadi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Azumi ta ce su ma ɗaurarrun daga cikin al'umma suka fito, saboda haka gwamnatin jihar za ta yi ƙoƙari wajen sama musu sauƙi a halin da suke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta buƙaci su yiwa Gwamna Yusuf addu'ar samun damar kawo roman dimokuraɗiyya ga mazauna jihar Kano.

Taimakon zai sanya farin ciki a fuskar daurarru

Da yake jawabinsa bayan karbar kayan abincin, shugaban kula da gidan gyaran halin na Kano, Sulaiman Inuwa ya ce kayan abincin zai ƙara zaburar da ɗaurarrun wajen zama ƴan ƙasa na gari bayan sun shaƙi iskar ƴanci.

Ya ce suna cikin shirin haɗa kai da gwamnatin Kano wajen tabbatar da adalci a jihar.

Sulaiman Inuwa ya mika godiya ga gwamnatin bisa kyautar kayan abincin ga daurarrun, wanda zai sanya farin ciki sosai a fuskokinsu.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya aika sako, ya taya Kanawa murnar kammala azumin Ramadan

Marasa laifi 300 aka daure a

A baya, rundunar 'yan sandan Kano ta ce mutane 300 ne ke daure a gidan ajiya da gyaran hali na Kurmawa ba tare da sun aikata laifin komai ba.

Kwamitin da Sufeta Janar na rundunar 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya kafa ne ya bankado hakan.

Kwamitin ya gano cewa wasu kuma tun da aka ajiye su a gidan ba a sake waiwayarsu ba na tsawon shekaru

Asali: Legit.ng

Online view pixel