Tinubu Ya Aika da Sako Mai Ratsa Zuciya Kan Rasuwar Jarumar Kannywood, Saratu Gidado Daso
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar jarumar Kannywood, Saratu Gidado Daso
- Shugaban ƙasan ya bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi ga masana'antar Kannywood da ƙasa baki ɗaya
- A saƙon ta'aziyyar wanda Ajuri Ngelale ya fitar a madadin Shugaba Tinubu, ya yi wa marigayiyar addu'ar Allah ya yi mata rahama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado Daso, wacce ta rasu a ranar Talata da safe a Kano.
Shugaban ƙasan ya aike da saƙon ta'aziyyar ne a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a shafin X.
Shugaban ƙasan ya aika da ta'aziyyarsa ga iyalan marigayiyar, masana'antar Kannywood, jihar Kano da duk wanda rasuwar jarumar ta taɓa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa za a yi kewar marigayiya Saratu Gidado bisa ayyukan bayar da agaji da take yi.
Me Tinubu ya ce kan rasuwar Saratu Gidado?
Ya bayyana rasuwarta a matsayin babban giɓi a masana'antar fina-finai ta Kannywood.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi ta'aziyya ga iyalai, abokan aiki da masoyan shahararriyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado, wacce ta rasu a ranar Talata da safe a Kano."
"Shugaban ƙasan ya bayyana rasuwar marigayiyar mai shekara 56 a matsayin abin baƙin ciki, ba ga waɗanda kawai suke jimamin rasuwarta ba amma har ga ƙasa baki ɗaya wacce ta karrama ta hanyar baiwar da take da ita."
"Shugaban ƙasan ya kuma aika da ta'aziyyarsa ga gwamnatin jihar Kano da duk waɗanda rasuwar Saratu Gidado ta taɓa yayin da yake yi mata addu'ar Allah ya yi mata rahama."
Tsohon alƙali ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon alƙalin kotun ɗaukaka ƙara, mai shari'a Ahmad Olanrewaju Belgore, ya riga mu gidan gaskiya.
Mai shari'a Belgore wanda ya yi ritaya daga kotun ɗaukaka ƙara a watan Afirilun 2023, ya yi bankwana da duniya ne yana da shekara 71.
Asali: Legit.ng