Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Jaruma Hadiza Gabon da aka gurfanar a Kotun Musulunci

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Jaruma Hadiza Gabon da aka gurfanar a Kotun Musulunci

Jarumar shirin Fim a Najeriya, Hadiza Aliyu, wacce ta shahara da Hadiza Gabon, ta ja hankali kwanan nan, ba don sana'arta na shirin Fim ba, sabida wani mutumi da ya kai ƙararta gaban Kotun Musulunci

A ranar 14 ga watan Yuni, 2022, aka shigar da ƙarar Hadiza Gabon a Gaban Kotu da niyyar zata halarci Kotun Shari'ar Musulunci dake Magajin Gari Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An zargi Jarumar da rashin cika Alƙawarin alaƙar soyayya da ta haɗa su da Wani ma'aikaci ɗan kimanin shekara 48, Bala Musa.

Rahoto ya nuna cewa Bala Musa, wanda ya maka ta a Kotun, ya bayyana cewa Gabon ta yi masa alƙawarin aure bayan ya kashe mata kuɗi da suka kai N396,000.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Atiku Abubakar ya zaɓi wanda yake so ya zama mataimakinsa a 2023

Sai dai da take kare kanta a Kotu, Jaruma Hadiza Gabon ta musanta yi wa mutumin alƙawarin aure kuma ta yi iƙirarin ba ta san shi ba sam.

Jaruma Hadiza Aliyu Gabon.
Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Jaruma Hadiza Gabon da aka gurfanar a Kotun Musulunci Hoto: @adizatou
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fitacciyar JarumaR ta jima ana damawa da ita masana'antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood Da takwararta ta kudancin Najeriya wato Nollywood.

Bugu da ƙari, Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa 5 da ya dace ku sani game da Gabon.

Abubuwa 5 game da Gabon

1. Hadiza Aliyu na da katin zama ɗan ƙasa na Najeriya da kuma Gabon. Mahaifinta Malam Aliyu ɗan Gabon ne yayin da mahaifiyarta yar Najeriya ce daga jihar Adamawa.

Gabon ta yi karatun Firamare da Sakandire duk a kasar da aka binne cibiyarta wato Gabon. Ta rubuta jarabawar shiga manyan makarantu a Gabon da burin karanta fannin shari'a amma ta jingine saboda wasu dalilai da ta barwa kanta sani.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

2. Hadiza Aliyu ta baro mahaifarta Gabon zuwa Najeriya domin cika burinta na zama fitacciyar Jaruma a 2009. Ta koma jihar Kaduna inda ta shiga masana'antar Kannywood.

Ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta fara shiga shirin fina-finai duk a 2009 lokacin da ta fito a fim mai suna 'Artabu'. Daga nan kuma ta yi tunanin faɗaɗa harkar fim ɗinta ta hanyar shiga Nollywood a 2017.

Jarumar ta fito a wani Fim mai suna, "Lagos Real Fake Life” tare da wasu fitattun jarumai kamar Emmanuella, Mike Ezuruonye, da Mark Angel da dai sauran su.

3. Daga shekarar 2013 zuwa 2019, Hadiza Gabon ta lashe kyaututtuka da dama da suka haɗa da 2013 Best of Nollywood, 2014 City People Entertainment, 2014 2nd Kannywood/MTN, da 2016 African Hollywood a matsayin Jaruma lamba ɗaya.

Haka nan kuma a shekarar 2013 ta samu kyautar giramawa daga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Mutanen Ebonyi sun fadawa Gwamnansu bai isa ya kinkimo masu Bola Tinubu a 2023 ba

4. Hadiza Gabon ta yi aiki a matsayin Ambasada ta Kamfanin Indomie noodles da MTN Najeriya. A watan Disamba, 2018, NASCON Allied PLC da ke karkashin Ɗangote Group ya sanar da Jarumar a matsayin Ambasadar kayan ɗanɗano yayin kaddamar da kayayyakin a Kano.

5. Gabon sananniya ce a fannin ayyukan jin ƙai da taimako, a 2016 ta kafa gidauniyar tallafawa gajiyayyu mai suna HAG Foundation.

Gidauniyar ta maida hankali wajen inganta rayuwar mutane masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar taimaka nusu a ɓangaren lafiya, Ilimi da kayayyakin Abinci.

A watan Maris, 2016, Fitacciyar jarumar ta ziyarci sansanin yan gudun hijira da ke Kano, inda ta tallafa musu da kayan abinci, tufafi da sauran kayayyakin da ƴan gudun hijira ke bukata.

A wani labarin kuma mun kawo muku yadda ta kaya bayan Jaruma Hadiza Gabon ta gurfana a gaban Kotun Musulinci kan tuhumar yaudarar aure

Jarumar ta faɗa wa Kotu cewa ba ta san mutumin ba, wanda ya kai ta ƙa ra bisa zargin ta masa alƙawarin aure bayan ya kashe mata kudi.

Kara karanta wannan

Kannywood: Jaruma Hadiza Gabon ta gurfana a gaban Kotun Musulinci kan tuhumar yaudarar aure

Gabon ta musanta tuhumar inda ta ce bata taba haɗuwa da shi ba kuma babu wata alaƙar soyayya a tsakanin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel