Mutanen Ebonyi sun fadawa Gwamnansu bai isa ya kinkimo masu Bola Tinubu a 2023 ba

Mutanen Ebonyi sun fadawa Gwamnansu bai isa ya kinkimo masu Bola Tinubu a 2023 ba

  • ‘Yan 'Association of Ebonyi Indigenes Socio-Cultural in Diaspora' sun aikawa David Umahi raddi
  • Kungiyar ta yi Allah-wadai da yadda Gwamnan na Ebonyi yake goyon bayan Bola Tinubu a 2023
  • Shugaban AEISCID ya fitar da jawabi yana mai cewa babu wanda ya isa ya kakaba masu Tinubu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ebonyi - Kungiyar Association of Ebonyi Indigenes Socio-Cultural in Diaspora ta mutanen Ebonyi da ke zama a kasar waje ta sha ban-bam da David Umahi.

This Day ta samu labari wannan kungiya ta yi wa Mai girma David Umahi raddi bayan Gwamnan ya fito yana tallata ‘dan takarar APC a zaben 2023, Bola Tinubu.

Kungiyar ta zargi Gwamnan na Ebonyi da cin amanar da ba a taba ganin irinsa a tarihin Najeriya ba.

Wannan kungiya ta AEISCID ta fitar da jawabin da shugabanta, Amb. Paschal Oluchukwu ya sa hannu a ranar Talata, ta na mai Allah-wadai da Gwamnan.

Kara karanta wannan

Abokin takara: Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna

Amb. Paschal Oluchukwu ya bayyana kalaman Umahi a matsayin abin takaici, bakin ciki da Allah-wadai, ya ce ba a taba samun wanda ya ci amana irinsa ba.

Nesanta kai daga Ohanaeze Ndigbo

Leadership ta ce wannan kungiya ta kuma soki yadda Gwamnan ya barranta daga jagorancin kungiyar Ohanaeze Ndigbo mai rajin kare hakkin mutanen Ibo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

David Umahi
David Umahi ya hadu da Bola Tinubu Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Jawabin da kungiyar ta fitar yake cewa Mai girma gwamnan ya nuna babu abin da ya shafe shi da harkar cigaban mutanensa na kabilar Ibo, sai dai ‘yan jiharsa.

Oluchukwu yace a wani irin yanayi mai ban mamaki, Umahi ya yi ikirarin shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo na kasa, George Obiozor, ba shugabansa ba ne.

A cewar Umahi, babu abin da ya hada shi da Farfesa George Obiozor ko ta kusa, ko ta nesa.

Jama'a su na neman yin bore

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Saka Labulle Da Lawan Da Ameachi a Aso Rock Villa

Abin da ya jawo wannan shi ne kalaman da suka fito daga bakin David Umahi, ya na mai cewa APC za a zaba a Ebonyi ba Jam’iyyar LP ta su Peter Obi ba.

Da yake nada Kwamishinoni da Hadimai a garin Abakaliki, Gwamnan na APC ya fada masu a 2023, APC za a zaba ba LP ba, hakan ya jawo masa suka ko ta ina.

NNPP da LP za su hada-kai?

Kun samu rahoto cewa jam’iyyar LP ta na tunanin dunkulewa tare da su Rabiu Musa Kwankwaso NNPP domin yakar Atiku Abubakar da Bola Tinubu a 2023.

Rabiu Musa Kwankwaso yana da mabiya birjik a Arewacin Najeriya, shi kuma Peter Obi ya na samun karbuwa musamman a yankin kudancin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel