Baki da ilimin addini - Fati Slow ta shigarwa sarkin waka, ta yiwa Nafisa Abdullahi wankin babban bargo

Baki da ilimin addini - Fati Slow ta shigarwa sarkin waka, ta yiwa Nafisa Abdullahi wankin babban bargo

  • Tsohuwar jarumar fim Fati Slow ta shiga rikicin da ya barke tsakanin Naziru Sarkin Waka da Nafisa Abdullahi kan almajirai
  • Slow ta ce Naziru ya yi gaskiya don babu wanda aka yi asarar haihuwarsa sama da wanda zai dunga iskanci yana nunawa duniya suna zagin iyayensa shi kuma yana dariya
  • Ta kuma bayyana cewa rashin cikakken ilimin addini ne ya sa har Nafisa ke zagin yaran da aka tura almajaranci

Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman da aka fi sani da Fati Slow ta fito ta goyi bayan caccakar abokiyar sana’arsu, Nafisa Abdullahi da Naziru Ahmad ya yi kan zagin iyayen da ke tura ‘ya’yansu almajiranci.

Fati Slow ta ce tabbass babu asararre sama da mutumin da zai dunga iskanci yana watsawa duniya ana zagin iyayensa amma ko a jikinsa.

Kara karanta wannan

Kullun burinka ka zagi yan fim: Maryam Booth ta yi martani ga Naziru sarkin waka

Tsohuwar jarumarta bayyana cewa sai inda karfinsu wajen fada ma duk mutumin da zai zagi almajirai gaskiya.

Baki da ilimin addini - Fati Slow ta shigarwa sarkin waka ta yiwa Nafisa Abdullahi wankin babban bargo
Baki da ilimin addini - Fati Slow ta shigarwa sarkin waka ta yiwa Nafisa Abdullahi wankin babban bargo Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

A wani bidiyo da ta saki a shafinta na Instagram inda a ciki ne ta yi shagube ga Nafisa, ta bayyana cewa jarumar bata da ilimin addini shi yasa har take iya kalubalantar tura yara almajiranci domin su koyo ilimin addininsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Naziru wannan maganarka gaskiya ne babu cikakken dan iska kuma wanda iyayensa ma basu san yadda za su yi da shi ba shine wanda zai yi iskanci ya turo duniya ana ta zagin iyayenshi yana dariya, shine cikakken dan iska.
“Kuma wanda yake ganin Naziru bai yi daidai ba, Naziru ya fito ya yi magana ka yi abun da za ka yi ko ki yi abun da za ki yi, ya fito nya fadi abun da ke ransa nima na fito na fadi abun da ke cikin raina.

Kara karanta wannan

Babu wacce iyayenta basu san yadda za su yi da ita ba sama da macen da za ta kama otel tana iskanci - Naziru

“Ai cikakkiyar jahila ce ke, abun da yasa nace cikakkiyar jahila c eke ai baki da ilimin addini, muma ba shi garemu ba don haka baki isa ki ci mutuncin almajiri ba, baki isa ki zagi almajiri ba. Zagin almajiri ba daidai bane kuma sai mun yi magana saboda ba tsoron wani muke ji ba.”

Tuni mabiya shafin nata suka tofa albarkacin bakunansu. Ga wasu daga cikin martanin nasu a kasa.

salihshamsiyya009

"Nafisa daureki zatayi ke tsohuwa idan naziru ya baki kudi saboda kin zageshi"

real_abdul_s_abdul ya yi martani:

“Naga allama wasu keburan kike so ya cire Miki daman kince 99 ya cire Miki Inga da akoy saura 1”

mubaraknasir121 ya ce:

“Wawuya kawai baki da aiki sai maula”

official_abk_blush yay i martani:

“Ke adole sai kinshiga abinda baruwanki”

Kullun burinka ka zagi yan fim: Maryam Booth ta yi martani ga Naziru sarkin waka

Kara karanta wannan

Mai neman suna: Idan ka isa ka bugi kirji ka kira suna, Nafisa ga Sarkin Waka

A baya mun kawo cewa shahararriyar jarumar Kannywood, Maryam Booth ta shiga sahun masu adawa da iyayen da ke tura yaransu wani waje da sunan almajiranci.

Sai dai Maryam ta yi shagube ne ga Naziru Sarkin Waka wanda ya fito ya caccaki masu adawa da tura yara almajiranci, harma ta kai ya kwancewa abokan sana’arsa zani kan haka.

Mawakin dai ya ce idan har ana neman wadanda iyayensu suka haife su amma suka kasa kula da su toh a tafi masana’antar fim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel