Da Farko Kallon Mahaukaci Ake Min: Mutumin Da Ya Zama Miloniya Da Sana'ar Sayar Da Ƙarafuna Masu Tsatsa Legas

Da Farko Kallon Mahaukaci Ake Min: Mutumin Da Ya Zama Miloniya Da Sana'ar Sayar Da Ƙarafuna Masu Tsatsa Legas

  • Wani dan Najeriya, Azeez Isma’il ya ce lokacin da ya fara sana’ar kyadi sai da ‘yan uwansa suka nuna rashin jin dadinsu akan sana’ar
  • Anguwar da ya koma don yin aikin nasa sun fara kiransa da mahaukaci har suka kai kararsa ga ma’aikatan gwamnati
  • Yayin da kuma ya samu arziki da sana’ar, nan da nan wadanda ke kallonsa a matsayin kazami suka fara kusantar shi don kulla zumunci

Wani dan Najeriya da ya zama miloniya da sana’ar kyadi inda ya ke sayar da karafa ya bayyana yadda mutane suka dinga yi masa kallon mahaukaci.

A wata tattaunawa da Sojuloore TV ta yi da shi, ya ce har karan-tsana aka daura masa a anguwar da ya ke zama suna masa kallon mahaukaci.

Mahaifina Ba Ya Son Sana'ar: Mutumin Da Ya Zama Miloniya Ta Sana'ar Kyadi Ga Wani Kamfani a Legas
Wasu suna min kallon mahaukaci da farko: Mutumin da ya zama miloniya ta hanyar sayar da karafa masu tsatsa. Hoto: YouTube/SOJULOORE TV.
Asali: UGC

Kara karanta wannan

N50m na ware tun farko, Minista ya fadi hanyar da zai tara N100m na sayen fam a APC

Azeez ya kara da cewa sai da wasu suka lakada masa duka ba tare da ya yi komai ba, inda ya nuna tabon ciwon da suka ji masa.

Yadda ya fara sana’ar

Mutumin ya ce ya yi wani bangare na kuruciyarsa a Abuja daga baya kuma ya koma gida wurin iyayensa kasancewar ya yi nisa sosai.

Bayan komawarsa gida ne ya ga masu tsintar karafa ya tambayesu amfanin da suke yi da shi. Sun sanar da shi cewa sayarwa su ke yi.

Daga nan sana’ar ta dauki hankalinsa. Duk da yadda ya ke samu da sana’ar, sai da mahaifinsa ya nuna cewa ba ya so.

Ubangiji ya daga shi

Mutumin ya shaida yadda ya ci gaba da tara karafan duk da kamfanin da ya ke kai mawa sun bukaci ya dakata. Ya tara karafa masu yawa.

A cewarsa, a lokacin masu sana’a irin tasa sun sauya salon neman kudi, nan da nan ya tara karafa masu yawa.

Kara karanta wannan

London zuwa Legas a babur: 'Dan Najeriya ya kai Spain, ya ci nisan 702km daga 12,000km

Ya ce Ubangiji ya yi masa budi ne bayan kamfanin sun neme shi, inda suka siya kaf karafan suka ba shi makudan kudade.

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A baya, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel