Karin bayani: Sabuwar dirama ya yin da fusatattun matasa suka mamaye majalisar dokokin jihar Filato

Karin bayani: Sabuwar dirama ya yin da fusatattun matasa suka mamaye majalisar dokokin jihar Filato

  • Da sanyin safiyar Litinin, matasa suka mamaye majalisar dokokin Filato domin zanga-zanga kan tsige kakaki
  • Duk da yawan jami'an tsaron dake wurin, fusatattun matasan sun yi wa wurin kawanya domin nuna ƙin amincewarsu
  • Tun a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne majalisa ta bayyana tsige Honorabul Abok, kuma ta maye gurbinsa da Sanda Yakubu

Plateau - Adadi mai yawa na matasa, ranar Litinin da safe, sun yi wa majalisar dokokin jihar Filato kawanya domin nuna fushinsu kan tsige kakakin majalisa, Abok Ayuba Nuhu.

Dailytrust ta rahoto cewa matasan sun tattaru ne a zauren majalisar da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin Litinin.

Rahoto ya nuna cewa duk da jami'an tsaro dake wurin, fusatattun matasan sun mamaye wurin domin zanga-zangar ƙin amincewa da tsige tsohon kakakin.

Matasa a majalisa
Da Dumi-Dumi: Matasa sun mamaye majalisar dokokin jihar Filato kan tsige shugaba Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sabon rikici a majalisa

Kara karanta wannan

Labari da ɗumi-ɗumi: Ortom ya kaiwa Orji Kalu ziyara a gidansa da ke Abuja

Sabuwar dirama a zauren majalisa na yau Litinin, inda tsohon kakakin majalisa da tawagarsa suka samu damar shiga zauren bayan hana su da aka yi ranar Alhamis, kamar yadda vanguard ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A zaman na yau, Tsohon kakakin wanda bai amince da tsige shi ba, ya dakatar da yan majalisu shida, waɗanda suka yi kutun-kutun aka cire shi daga muƙaminsa.

A ranar Alhamis da ta gabata ne aka tsige Honorabul Abok, kuma aka maye gurbinsa da Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazaɓar Pengana, karamar hukumar Bassa.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Naanlong Daniel, wanda ya jagoranci tsige kakakin, yace mambobi 16 cikin 24 sun sa hannun amince wa da lamarin.

Shin tsohon kakakin ya amince da tsige shi?

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa Honorabul Abok ya yi watsi da lamarin tsige shi da yan majalisun suka yi.

Kara karanta wannan

Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

Ya bayyana cewa lamarin ya saɓa wa doka domin kashi 2 cikin 3 na mambobin majalisan ba su sa hannun amincewa da cire shi ba.

Jim kaɗan bayan tsige shi a ranar Alhamis, tsohon kakakin ya gudanar da zaman majalisar tare da mambobin dake goyon bayansa a Zawan dake ƙaramar hukumar Bassa.

A wani labarin kuma mun kawo muku babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP

Rahoto ya bayyana cewa Jonathan ya faɗa wa gwamnonin PDP biyu da suka ziyarce shi cewa ba zai halarta ba saboda zai bar Najeriya.

Gwaamnonin sun roki babban jigon na PDP da ya halarci wurin kuma ya bada jawabinsa kafin ya kama hanyar fita kasar, amma ya watsa musu ƙasa a ido.

Asali: Legit.ng

Online view pixel