'Ba da Mu ba': Iran Ta Sake Gindaya Sharudan Tsagaita Wuta a Yaki da Isra'ila
- Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce kasar ba ta neman tsagaita wuta yayin da Amurka ke cewa suna tattaunawa
- Sai dai Araghchi ya bayyana abu daya da za su iya amincewa da shi ba tare da matsala ba a yakin da ake yi
- Ya bayyana cewa hulda da Amurka ba tattaunawa ba ce kai tsaye, illa musayar sakonni kawai, kai tsaye ko ta hannun kasashen yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi magana kan kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
Araghchi ya bayyana cewa Iran ba ta neman tsagaita wuta, sai dai cikakken kawo karshen yaki a yankin.

Source: Getty Images
Sharadin Iran kan tsagaita wuta a yakin Isra'ila
Ministan ya jaddada cewa duk wani sulhu dole ya hada da tabbacin hana hare-hare a gaba da kuma biyan diyya kan barnar da aka yi, cewar Anadolu Ajansi.
Araghchi ya ce hulda da Amurka ba tattaunawa ba ce, illa musayar sakonni kai tsaye ko ta hannun wasu kasashen yanki.
Ya shaida wa Al Jazeera cewa yana ci gaba da karbar sakonni daga wakilin Amurka Steve Witkoff kamar yadda aka saba a baya.
Sai dai ya jaddada cewa wannan bai kamata a dauke shi a matsayin tattaunawa ta hukuma tsakanin kasashen biyu ba a wannan lokaci.
Ya kara da cewa sakonnin na zuwa ne ta ma’aikatar harkokin waje, tare da wasu mu’amala tsakanin hukumomin tsaro daban-daban.
Ya ce babu wata tattaunawa kai tsaye da wani bangare na musamman a cikin Iran, dukkan hulda tana karkashin tsari na gwamnati.
Araghchi ya bayyana cewa ana gudanar da musayar sakonnin karkashin kulawar Majalisar Tsaron Kasa ta Iran a matsayin tsari na hukuma.
Ya kara da cewa sakonnin sun hada da gargadi da bayyana ra’ayoyi daga bangarorin biyu, ta hanyoyi na musamman da aka tsara.

Source: Getty Images
Matsayar Iran kan sharudan Trump 15
Dangane da rahotannin cewa Iran ta mayar da martani kan sharuda 15 na Amurka, ya ce ba a aika da wani martani ba har yanzu.
Ya ce Tehran ba ta gabatar da wata shawara ko sharadi ba, kuma babu wani mataki da aka dauka kan batun tattaunawa a yanzu.
Araghchi ya jaddada cewa al’ummar Iran ba za a iya tsoratar da su ba, yana kira ga shugaban Amurka da ya mutunta kasar.
Kan batun tsaron teku, ya ce mashigin Hormuz yana bude gaba daya, kuma za a takaita shi ne kawai ga masu kai hari kan Iran.
Ya kara da cewa an dauki matakai domin tabbatar da tsaron jiragen kasashen kawaye da suke wucewa ta wannan muhimmiyar hanya ta ruwa.
Isra'ila za ta mamaye Lebanon
An ji cewa ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ya yi magana kan shirin da Isra’ila ke yi na mamaye wasu yankunan kudancin Lebanon.
Katz ya bayyana kudirin kafa yankin tsaro har zuwa kogin Litani tare da ci gaba da ikon tsaro domin fadada ikonta.
Ya ce za a hana mazauna yankin dawowa, tare da rusa gidaje kamar yadda aka yi a Gaza wanda ya jawo magana.
Asali: Legit.ng

