Shugaba Pezeshkian Ya Gano Masu Goyon Bayan Iran a Yaki da Amurka, Ya Aika Masu Sako

Shugaba Pezeshkian Ya Gano Masu Goyon Bayan Iran a Yaki da Amurka, Ya Aika Masu Sako

  • Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya fahimci irin kauna da goyon bayan da al'ummar Iraki ke nuna wa Jamhuriyar Musuluncinta a yakinta da Amurka/Isra'ila
  • Masoud Pezeshkian ya yaba da wannan goyon baya da Iran ke samu daga Iraki, tare da tura sakon fatan alheri da godiya da jama'ar kasar
  • Haka zalika an ga motocin dakarun rundunar PMF na shiga cikin kasar Iran bayan Amurka ta yi barazanar tura sojojin kasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana godiyarsa ga al’ummar Iraki bayan da hukumomin Iran suka karbi wasu ayarin motocin mayakan Iraki a cikin kasar a wannan makon.

Hakan na zuwa ne bayan Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi barazanar tura dakarun sojojin kasa zuwa cikin Iran domin kwace wasu muhimman wurare na man fetur.

Kara karanta wannan

Amurka da Isra'ila sun sake tafka babbar asara a yaki da Iran da aka kakkabo jirgin MQ 9

Shugaban Iran.
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian a wurin taron kasa da kasa Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X, Pezeshkian ya ce al’ummar Musulmi na Iraki sun tsaya tsayin daka tare da Iran a wannan yaki da ya kira na rashin adalci.

Shugaban kasar Iran ya ce:

“Al’ummar Musulmi na Iraki sun tsaya tare da Iran cikin jarumtaka a wannan yaki. Wannan ba wai saboda kusanci da makwaftaka ta kasa ba ne kawai, har ma saboda tarihi, asali da kuma hadin kan addini.”

Iran ta tura sakon godiya ga al’ummar Iraki

Shugaban ya kara da cewa yana mika gaisuwa da godiya ga al’ummar Iraki, shugabanninsu da kuma mayakansu, yana mai nuna jin dadinsa kan irin goyon bayan da suka bayar.

Bidiyoyi da kafafen yada labarai na Iran da Iraki suka yada sun nuna ayarin motocin mayakan kungiyar Popular Mobilisation Forces (PMF), wacce ke da alaka da Iran, suna shiga cikin kasar.

Rahoton tashar Al-Jazeera ya bayyana wannan mataki na tura mayaka zuwa Iran a matsayin “ayarin taimakon jin kai na farko daga al’ummar Iraki.”

Kara karanta wannan

Tchiani ya tsoma baki a yakin Iran da Isra'ila, yana zargin an kulla wa Nijar makirci

Me yasa Iraki ta tura dakaru zuwa Iran?

Ana ganin wannan taimako da Iraki ta tura Iran ba zai rasa nasaba da barazanar Shugaban Amurka, Donald Trump na tura dakarun sojojin kasa zuwa cikin kasar ta Musulunci ba.

Shugaba Trump ya fito fili ya bayyana cewa zai so Amurka ta kwace iko da duk wasu albarkatun mai na kasar Iran tare da kwace sinadarin Uranium da kasar ta mallaka.

Sojojin Iran.
Dakarun rundunar sojojin kasar Iran suna tsakiyar fareti Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Wannan lamari na kara nuna karfafa alaka tsakanin Iran da Iraki, musamman a wannan lokaci na rikici, inda kasashen ke kara hadin kai bisa dalilai na addini da siyasa.

Shugaba Trump na tunanin tura sojoji Iran

A baya, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump na duba yiwuwar kaddamar da wani farmakin sojan kasa kan kasar Iran.

Wani rahoto ya gano Trump na son a kai harin domin kwashe kusan fam 1,000 na sinadarin uranium da ake hada makamin nukiliya da shi daga ƙasar Iran.

Majiyoyi sun ce har yanzu Trump bai yanke hukunci na ƙarshe a kan lamarin ba, yana ci gaba da auna haɗarin da irin wannan aiki zai iya haifar wa sojojin Amurka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262