Sanata Ya Fara Kumfar Baki da Saudiyya, UAE Suka Ki Taya Amurka Yakar Iran

Sanata Ya Fara Kumfar Baki da Saudiyya, UAE Suka Ki Taya Amurka Yakar Iran

  • Sanata Lindsey Graham ya soki abokan hukdartAmurka a yankin Gulf kan kin shiga yaƙin da ake yi da Iran
  • Ya nuna rashin jin daɗinsa da matakin UAE na hana amfani da ƙasarta wajen kai hare-hare a kan Iran
  • Graham ya kuma soki Spain kan kin barin Amurka ta yi amfani da sansanonin sojinta wajen kai makamantan harin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States –Sanata a jam’iyyar Republican a Amurka, Lindsey Graham, ya bukaci abokan hulɗar Amurka a yankin Gulf su ƙara himma wajen goyon bayan ƙasarsa da Isra’ila a rikicin da ke tsakaninsu da Iran.

Graham ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda wasu ƙasashen da ke kawance da Amurka suka ƙi shiga yaƙin ko kuma bayar da goyon baya kai tsaye.

Kara karanta wannan

Ana musayar wuta, Trump ya fadi abin da zai kawo karshen yakin Amurka da Iran

Graham ya soki ƙasashen da suka ki amincewa a yaki Iran tare
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, Sanata a Amurka Lindsay Graham Hoto: Masoud Pezeshkian/Lindsay Graham
Source: Facebook

Al-Jazeera ta wallafa cewa Sanatan ya ce matakin da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ɗauka na hana amfani da ƙasarta wajen kai hare-hare kan Iran ya ba shi takaici matuƙa.

Sanata Amurka ta nemi ɗaukin kasashen Larabawa

Middleeast eye ta ruwaito a cewar Graham, Amurka na bukatar abokan hulɗar da za su iya tashi tsaye su goyi bayan ƙasar a lokacin da ake fama da irin wannan rikici mai muhimmanci.

Ya bayyana mamaki a kan matsayar da ƙasashen suka dauka, inda ya ce za su ga sakamakon rashin taya Amurka da Isra'ila yaki.

Sanatan Amurka ya ce kasashen da suka ki taya su yakar Iran za su gani
Shugaban Amurka Donald J Trump Hoto: Getty
Source: Getty Images

Ya ce:

"Muna bukatar abokan hulɗa da za su fito su mara mana baya a yaƙin da ba za mu iya yin sakaci mu yi rashin nasara a ciki ba.”

Sanatan ya ƙara da cewa yana sa ran ƙasashen da Amurka ke abota da su, musamman Saudiyya da sauran ƙasashen yankin Gulf, za su fito su nuna cewa su ma suna da ruwa a cikin wannan rikici.

Kara karanta wannan

Switzerland ta tsoma baki a yakin da Isra'ila da Amurka suka ƙaddamar a kan Iran

A cewarsa:

“Ina so abokanmu a Saudiyya da sauran ƙasashe su fito su ce, ‘Wannan fa yaƙina ne ma.’”

Sanatan Amurka ya gorantawa ƙasashen Larabawa

Graham ya kuma tunatar da ƙasashen Larabawa cewa Amurka ta yi ƙoƙari sosai wajen taimaka musu wajen gina sabon tsarin siyasa da tsaro a Gabas ta Tsakiya.

Ya ce:

“Ga abokanmu Larabawa, mum yi ƙoƙari wajen taimaka muku gina sabon Gabas ta Tsakiya. Ya kamata ku ƙara ƙaimi a wannan lokaci.”

Baya ga ƙasashen Gulf, Graham ya kuma soki Spain kan matakin da ta ɗauka na hana Amurka amfani da wasu sansanonin soji da suke tare domin gudanar da yaƙi da Iran.

Spain ta bayyana cewa ba za ta amince a yi amfani da sansanonin sojin da Amurka ke da su a ƙasarta wajen kai hare-hare kan Iran ba.

Graham ya ce wannan mataki ba shi da daɗi daga ƙasar da ake ɗauka a matsayin kawar Amurka.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 7, Iran ta sauya salon yaki da Amurka, ta sassautawa Larabawa

Saboda haka ya ba da shawarar a mayar da jiragen yaƙin Amurka da ke cikin waɗannan sansanoni zuwa ƙasashen da za su ba su damar amfani da su idan bukatar hakan ta taso.

Sanatan ya ƙara da cewa ya kamata a mayar da jiragen zuwa ƙasar da za ta ba Amurka damar amfani da su idan ta fuskanci barazana daga wata gwamnati irin ta Iran.

Gargadin Amurka ga Iran

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sabon jagoran addinin Iran ba zai daɗe a mulki ba idan bai samu amincewar Amurka ba

Donald Trump ya yi zargin cewa Iran na shirin mamaye Gabas ta Tsakiya baki ɗaya yayin da ƙasarsa da Isra'ila suka fara kai mata harin da ya hallaka jagoranta, Ali Khamenei

Shugaban ya kuma ce Amurka ba ta cire yiwuwar tura sojojin musamman domin kwace sinadarin uranium da ake ganin za a iya amfani da shi wajen samar da makamin nukiliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng