Yakin Iran/Isra'ila: An Rufe Masallatai tare da Umarnin Dakatar da Sallar Juma'a

Yakin Iran/Isra'ila: An Rufe Masallatai tare da Umarnin Dakatar da Sallar Juma'a

  • Kasar Isra’ila ta soke sallar Juma’a a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke Kudus, tana danganta matakin da matsalolin tsaro
  • Shugaban hukumar kula da fararen hula ta Isra’ila, Birgediya Janar Hisham Ibrahim, ya ce hukumomi sun yanke shawarar rufe wuraren ibada saboda tsoron tabarbarewar tsaro
  • Ya ƙara da cewa duk wuraren ibada a tsohon birnin Kudus za su kasance a rufe, kuma ba za a bari masu ibada ko baƙi su shiga ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Kasar Isra’ila ta dauki matakai masu tsauri game da ibada saboda halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kasar ta soke gudanar da sallar Juma’a a harabar Masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus yayin da ake ci gaba da kai ruwa ranar tsakanin Iran da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Iran ta harba makamai masu linzami kan babban birnin Isra'ila, an ji barnar da suka yi

Isra'ila ta hana sallar Juma'a a masallacin Kudus
Musulmai sun taru a masallacin Kudus (Al-Aqsa) a ranar Juma'a ta biyu ta Ramadan. Hoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu.
Source: Getty Images

Hukumar kula da harkokin fararen hula ta Isra’ila ta sanar da matakin saboda maslahar tsaro, cewar rahoton Al Jazeera.

Yadda yakin Iran da Isra'ila ya barke

Duka wannan matakai da ake dauka na zuwa ne bayan barkewar rikici tsakanin Iran da Isra'ila a karshen makon da ya gabata.

A ranar Asabar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026, Isra'ila ta kai wani mummunan hari a Iran tare da hadin guiwar kasar Amurka.

Harin da aka kai ya yi sanadin rasa ran jagoran addinin Musulunci a Iran, Ayatollah Ali Khamenei wanda ya jawo fargaba da tsoron abin da ka iya biyo baya.

Daga bisani, Iran ta sha alwashin daukar fansar jinin shugabanta tare da fara shirin yaki da ta ce ba ta san ranar karewarsa ba.

Isra'ila ta rufe masallatai saboda rikici a Gabas ta Tsakiya
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Musabbabin hana sallar Juma'a a masallacin Kudus

Hukumar ta danganta matakin da matsalolin tsaro yayin rikicin Amurka, Isra’ila da Iran ke ci gaba da ta'azzara.

Kara karanta wannan

Rasha ta fadi dalilin da ya sa ba ta kai dauki ga Iran ba a yakinta da Isra'ila

Ta ce an yanke shawarar domin dakile yiwuwar tashin hankali a wuraren ibada da kuma tsaron al'umma wanda shi ne abu mafi muhimmanci.

Shugaban hukumar, Birgediya Janar Hisham Ibrahim, ya ce:

“Dukkan wuraren ibada da ke tsohon birnin Kudus, ciki har da Western Wall, Temple Mount da Cocin Holy Sepulchre, za su kasance a rufe gobe.”
“Ba za a bari masu ibada ko baƙi daga kowane irin addini su shiga wuraren ba."

Ya tabbatar da cewa hukumomi na ci gaba da sa ido kan halin tsaro a kasar baki daya domin sake samun dabaru da za su kare al'umma.

Falasɗinawa: Trump ya juya wa Isra'ila baya

A baya, an ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana adawarsa ga shirin Isra’ila na kara mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da Falasdinawa ke zaune a ciki.

Wani jami’in Fadar White House ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Kogin Jordan na da muhimmanci wajen kawo zaman lafiya.

Kasashen Musulmi da dama, majalisar dinkin duniya da wasu kasashen Turai sun yi kakkausar suka kan matakan mamaya da Isra'ila ke dauka a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.