Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Yahudawa sun kai mummunan hari Masallacin Kudus

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Yahudawa sun kai mummunan hari Masallacin Kudus

- Wasu Yahudawa masu tsautsauran ra'ayi sun kai hari masallacin Aksa dake gabas da Kudus

- Yahudawan sun shiga masallacin ne ta kofar Al-Magrib tare da jami'an tsaro dake take musu baya

- Ba wannan ne karo na farko ba da aka fara kai hari masallacin ba, don an saba rikici tsakanin Falasdinawa da jami'an tsaron Isra'ilawa

Wasu Yahudawa masu tsaurin ra'ayi sun kai hari masallacin Aksa dake gabashin Kudus. Sun kutsa cikin masallacin tare da jami'an tsaro masu kula da lafiyarsu.

Sanarwar kai harin ta fito ne daga ofishin asusun kula da Masallacin, inda aka bayyana cewa Yahudawan kimanin su dari da talatin ne suka kai wannan harin. Suna tafe ne tare da jami'an 'yan sandar kasar masu kula da lafiyarsu.

Jaridar TRT ta kasar Turkiyya ta bayyana cewa, Yahudawan sun kai harin ne ta kofar Al-Magrib, daya daga cikin kofofin masallacin inda suka rufarwa mutanen dake ciki.

KU KARANTA: Yadda mijin mahaifiyata ya nemi lalata dani lokacin da nake dauke da ciki - Jaruma

Hakazalika, sanarwar da ta fito daga ofishin asusun kula da masallacin ta bayyana cewa, a cikin wadanda suka kai farmakin akwai sojoji mata sanye cikin khaki.

Wannan kuwa ba shi ne karo na farko ba da Yahudawan suka fara kai irin wannan farmakin masallacin.

Irin wannan hare-haren kuwa na kawo matsala tsakanin Falasdinawa da kuma jami'an tsaron kasar Isra'ila.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel