Kotun Koli Ta Dakile Yunkurin Trump, Ta Yi Watsi da Dokokin Haraji da Za Su Shafi Duniya

Kotun Koli Ta Dakile Yunkurin Trump, Ta Yi Watsi da Dokokin Haraji da Za Su Shafi Duniya

  • Kotun Koli ta soke harajin da Donald Trump ya kakaba, ta ce bai da hurumin yin hakan ba tare da amincewar Majalisar Amurka ba
  • Kotun ta ce dokar gaggawa da aka dogara da ita ba ta bai wa shugaban kasa ikon sauya tsarin kasuwancin duniya shi kadai ba
  • Hukuncin zai iya jawo kamfanoni su nemi mayar da biliyoyin daloli da suka biya, tare da kara muhawara kan iyakar ikon shugaban kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Kotun Koli a Amurka ta yi hukunci game da korafin da aka shigar kan kakaba haraji da Shugaba Donald Trump ya yi.

Kotun ta soke wani muhimmin bangare na manufofin tattalin arziki na Donald Trump, inda ta yanke cewa dokar da ya dogara da ita ba ta ba shi ikon kakaba manyan haraji kan kayayyakin shigo da kaya ba.

Kara karanta wannan

Iran ta ki tsorata da barazanar Trump, ta fadi illar da za ta yi wa Amurka

Kotun Koli ta yi wa Trump illa a shirin haraji
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

Kotu ta yi fatali da harajin Trump a kasashe

A hukuncin kuri’a shida da uku, Babban Alkalin kotun, John Roberts, ya bayyana cewa akwai tanadin kundin tsarin mulki game da dokar, cewar CNN.

Ya ce kundin tsarin mulki ya tanadi cewa dole ne Majalisa ta bayar da cikakkiyar izini kafin shugaban kasa ya yi amfani da irin wannan babban iko a fannin tattalin arziki.

Kotun ta bayyana cewa ba aikin ta ba ne tantance ko haraji yana da amfani ko a’a, sai dai ta tabbatar da iyakar ikon bangaren zartarwa.

Ta ce shugaban kasar Amurka ba zai iya kakaba haraji mai girma haka ba tare da sahihin izini daga Majalisa ba.

Kotu ta kawowa Trump tsaiko kan kakaba haraji
Shugaba Donald Trump yayin kamfen zabe da ya yi nasara. Hoto: @RealDonaldTrump/X.
Source: Twitter

Kasashen da harajin Trump ya shafa

Rahotanni sun nuna cewa harajin da aka kakaba sun shafi kasashe kamar Canada, China da Mexico ya samar da biliyoyin daloli, amma ya kara tsadar kaya ga kamfanoni da masu saye.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: An taso gwamnati a gaba bayan hukuncin kisa ga Aminu Sheriff

Yanzu ana sa ran kamfanoni da dama za su nemi a mayar musu da kudaden da suka biya, cewar BBC.

Alkalin ya ce:

“Shugaban kasa yana ikirarin wani sabon iko na musamman na kakaba haraji shi kadai ba tare da iyaka ba, ko ta fuskar adadi, tsawon lokaci ko fadin tasiri.
“Dangane da girma, tarihin da kuma muhallin kundin tsarin mulki na wannan ikon da ake ikirari, dole ne ya nuna karara sahihin izini daga Majalisa kafin ya yi amfani da shi.”

Hukuncin ya zama babbar koma baya ga Trump, tare da kara tayar da muhawara a Washington kan daidaiton iko tsakanin Majalisa da Fadar White House, musamman game da amfani da dokokin gaggawa a lokutan zaman lafiya.

Nukiliya: Trump ya ba Iran wa'adin mako 2

A wani labarin, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ba ƙasar Iran wa’adin kwanaki 10 zuwa 15 game da yarjejeniyar da suke shirin kullawa.

Trump ya ce idan tattaunawa ta gaza, sakamakon zai kasance “mafi muni” ga Iran, yana mai jaddada cewa dole ne a samu mafita ta kowace hanya.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce an samu ci gaba amma ba za a kai ga matsaya cikin gaggawa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.