InnalilLahi: Bam Ya Tarwatse a Masallacin Juma'a, An Rasa Rayukan Musulmai 31
- Wani dan kunar-bakin-wake ya kashe masallata 31 tare da jikkata wasu 169 bayan ya tayar da bam a babban birnin Pakistan a ranar Juma'a
- Wannan harin ya faru ne a wani masallacin mabiya mazhabar Shi'a da ke yankin Tarlai a daidai lokacin da suke gabatar da Sallar Juma'a
- Shugaban kasa da Firayiministan Pakistan sun bayyana harin a matsayin babban laifi ga dan adam yayin da aka ayyana dokar ta-baci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Pakistan - Aƙalla mutane 31 ne aka tabbatar sun mutu, yayin da wasu 169 suka ji raunuka bayan wani harin ƙunar-bakin-wake a Islamabad.
Harin ya faru ne a wani masallacin mabiya mazhabar Shi'a dake yankin Tarlai yayin da ake gudanar da sallar Jumu'a a yau, 6 ga Fabrairu, 2026.

Source: Getty Images
Wannan shi ne hari mafi muni da ya girgiza ƙasar tun bayan fashewar bam a masallacin Peshawar a watan Janairun shekarar 2023, a cewar rahoton CNN.
Pakistan: Bam ya tarwatse a masallaci
Mazauna yankin sun bayyana cewa masallacin ya cika maƙil da mutane sama da 400 lokacin da maharin ya tada bam ɗin.
An fara jin ƙarar harbe-harben bindiga na ɗan lokaci kafin wata gagarumar fashewa ta biyo baya wadda ta ruda masallatan.
Syed Ameer Hussain Shah, mai shekaru 47 wanda ya tsira daga harin, ya ce:
“Muna fara sallah muka ji ƙarar harbi, sannan fashewa ta biyo baya.”
Ya ƙara da cewa:
“Na ji rauni ni ma. A lokacin babban zauren masallacin ya cika makil da masallata sama da mutum dari hudu.”
Halin da ake ciki bayan tashin bam
Hukumomin birnin Islamabad sun ayyana dokar ta-ɓaci a dukkan asibitoci domin ba wa waɗanda suka ji rauni kulawar gaggawa.
Irfan Memon, Mataimakin kwamishinan birnin, ya tabbatar da cewa adadin mutanen da suka mutu na iya ƙaruwa saboda raunukan da wasu suka ji.
Hotunan bayan harin sun nuna ɓarnar da aka yi, inda gawarwaki da jini suka mamaye cikin masallacin dake cike da baraguzan gine-gine.

Kara karanta wannan
Sarki ya fasa ƙwai, ya faɗi kuskuren sojoji, DSS da ya jawo kisan mutum 75 a Kwara
Wani mai ɗaukar hoto na kamfanin dillacin labarai na AFP ya bayyana cewa ya ga daruruwan mutane suna isa asibiti cikin mawuyacin hali.
Kungiyar Taliban ta musanta kai hari
Duk da cewa jami'an tsaro sun fara zargin ƙungiyar Taliban ta Pakistan (TTP) da kai harin, ƙungiyar ta fito ta musanta hannunta a harin.
A cikin wata sanarwa, TTP ta ce:
“Ba mu da wata alaƙa da harin na yau. Wuraren harinmu a bayyane suke; hukumomin tsaro ne.”
Harin ya girgiza birnin Islamabad wanda aka sani da tsauraran matakan tsaro, inda ko a watan Nuwamba an kai wani harin, cewar wani rahoto na BBC.
Hukumomin tsaro sun rufe dukkan hanyoyin dake kai wa yankin na Tarlai domin gudanar da bincike kan yadda maharin ya ratsa jami'ai.

Source: Getty Images
Martanin shugabannin Pakistan da na duniya
Shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, ya bayyana harin a matsayin "laifi ga ɗan adam" wanda daukacin al'ummar ƙasa ke Allah-wadai da shi.
Firayim Minista Shehbaz Sharif ya nuna matuƙar juyayi, yana mai bayyana cewa gwamnati za ta kamo duk waɗanda ke da hannu a ta'addancin.
Bam ya tashi a masallaci a Borno
A wani labari, mun ruwaito cewa, wani abin fashewa (IED) da ake kyautata zaton bam ne ya tashi da mutane a masallaci ana cikin sallar Magariba a jihar Borno.
Wani dan kunar bakin wake ne ya tashi bam din da misalin karfe 6:00 na yammaci a wani masallacin Gamboru a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Wasu da suka tsira daga harin sun ce maharin ya shige cikin masallacin ne a ɓoye, sannan ya tayar da bam a lokacin da ake tsaka da sallar Magariba ta jam’i.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

