Da Duminsa: Taliban da sanar da sabon shugaba da sabbin ministoci

Da Duminsa: Taliban da sanar da sabon shugaba da sabbin ministoci

  • Kungiyar Taliban ta nada Mullah Mohammad Hassan Akhund a matsayin sabon Farai Minista na kasar Afghanistan
  • Zabihullah Mujahid, mai magana da yawun kungiyar ta Taliban ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar
  • Taliban ta kuma nada wasu sabbin ministocin rikon kwarya cikinsu har da Mullah Yaqoob dan tsohon shugaban Taliban Mullah Omar

Afghanistan - Kungiyar Taliban ta sanar da Mullah Mohammed Hassan Akhund a matsayin sabon shugaban gwamnatinta a Afghanistan a yau Talata, The Punch ta ruwaito.

Babban mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid ya shaidawa manema labarai ya sanar da cewa wanda aka kafa Taliban da shi Abdul Ghani Baradar shine zai zama mataimakin shugaban kungiyar.

Da Duminsa: Taliban da sanar da sabon shugaba da sabbin ministoci
Sabon shugaban kungiyar Taliban, Mullah Mohammad Hassan Akhund. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

Su wanene sabbin ministocin da Taliban da nada?

A cewar kakakin na Taliban sabon ministan harkokin cikin gida shine Sarajuddin Haqqani kamar yadda LIB ta ruwaito.

Sauran nade-naden sun hada da Mullah Yaqoob a matsayin ministan tsaro na riko, Amir Khan Muttaqi a matsayin ministan riko na harkokin kasashen waje sai Mullah Abdul Ghani Baradar and Mullah Abdul Salam Hanafi a matsayin mataimakansa biyu.

Yaqoob shine dan wanda ya kafa Taliban marigayi Mullah Omar.

A baya, Baradar ne shugaban ofishin siyasa na Taliban wanda ya ratabba hannu kan yarjejeniya da Amurka na ficewa daga kasar a bara.

Sabon ministan harkokin cikin gidan yana jerin mutanen da FBI ke nema ruwa a jallo duba da shine shugaban kungiyar masu tada kayar baya na Haqqani wadanda ke da alaka da Taliban kuma sun kai hare-hare da dama yayin yakin da aka shafe kimani 20 ana gwabzawa.

Taliban ta kwace mafi yawancin sassan kasar kimanin makonni uku da suka gabata, ta hambarar da tsohon zabebben shugaba Ashraf Ghani.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: An bayyana jigon PDP da ya shirya sosai don kwace mulki daga APC

Kakakin na kungiyar Taliban, Zabihullah Mujahid ya kara cewa kungiyar ta amsa bukatan mutane yana mai cewa:

"Mun san mutanen kasar mu sun dade suna jiran ganin sabuwar gwamnati."

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya sallami ministoci biyu daga cikin yan fadarsa da ya zaba a ranar 21 ga watan Agustan 2019.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta ce bukatar 'sabon jini' ne yasa aka yi sauyin ministocin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An maye gurbin su da Dr Mohammed Mahmood Abubakar, Ministan Muhalali da Abubakar D. Aliyu, Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164