Akidar Shi'a ba musulunci ba ne, inji Shekau

Akidar Shi'a ba musulunci ba ne, inji Shekau

Kungiyar Boko Haram bangaren Abubakar Shekau ta fitar da wani sabon hoton bidiyo, a inda Shekau ya ja hankalin mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya da kuma jagoransu, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da cewa su tuba domin abin da suke yi ba Musulunci ba ne.

Ya kuma kara da cewa tafarkin da 'yan Boko Haram suke bi ne kawai mafita ga mabiya mazhabar ta Shi'a. Shekau ya kuma karyata sojojin Najeriya cewa sun raunata shi.

KU KARANTA: Kungiyar CNPP na neman Yakubu Dogara ya sauka

A cikin sabon bidiyon wanda kungiyar ta fitar da sanyin safiyar ranar Lahadi, Abubakar Shekau ya kwashe kimanin minti 40 yana magana da harsunan Hausa da Larabaci da kuma Kanuri.

Da fari dai ya karyata rundunar sojin Najeriya da ta bayar da sanarwar raunata shi a wani harin sama da ta ce ta kai kan 'yan Boko Haram.

Shekau ya ce yana nan lafiya kalau babu abin da ya same shi.

Baya ga karyata sojojin, Abubakar Shekau ya bayyana Najeriya da kasar kafirci, a inda ya rera taken Najeriya da Turanci, bayan ya bayyana shi da wata alama ta kafirci.

Ya kuma sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a Najeriya, har zuwa lokacin da kasar za ta koma kan tafarki irin nasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng