Mutuwar Aure: Attajirin Duniya Ya Tura wa Tsohuwar Matarsa Naira Tiriliyan 11.47
- Bill Gates ya tura dala biliyan 7.88 (kusan Naira tiriliyan 11.47) ga gidauniyar tsohuwar matarsa Melinda, shekaru bayan rabuwarsu
- Wannan tallafi na daga cikin yarjejeniyar dala biliyan 12.5 da suka kulla lokacin da Melinda ta bar gidauniyarsu ta Bill & Melinda Gates
- Melinda French Gates za ta yi amfani da wadannan kudade ne wajen gudanar da ayyukan samar da jin kai da tallafi ga matan duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Wanda ya kafa kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya tura adadin kuɗi har dala biliyan $7.88 ga gidauniyar tsohuwar matarsa, Melinda French Gates.
Wannan tallafi na daga cikin gagarumar yarjejeniyar saki da suka ƙulla domin ba Melinda damar ci gaba da ayyukanta na jin ƙai daban da gidauniyar Bill & Melinda Gates Foundation da suka kafa tare a shekarar 2000 don yaƙar talauci da cututtuka a duniya.

Kara karanta wannan
Harin Amurka: Shugaban ƙaramar hukuma a Binuwai ya nemi ɗauki kan karuwar ƴan ta'adda

Source: Twitter
Bill Gates ya tura wa matarsa $7.88bn
Binciken bayanan haraji da jaridar New York Times ta wallafa ya nuna cewa an tura waɗannan kuɗaɗen ne a shekarar 2024 zuwa gidauniyar Pivotal Philanthropies Foundation, wata ƙungiya mai zaman kanta da Melinda ta ƙaddamar bayan rabuwarsu.
Melinda ta yi murabus daga gidauniyar Gates ne a watan Mayun 2024, inda ta bayyana cewa a ƙarƙashin yarjejeniyarta da Bill, tana sa ran karɓar ƙarin dala biliyan $12.5 don mayar da hankali kan ayyukan da suka shafi mata da iyalai.
Wakilin Melinda ya tabbatar da cewa: “An cika yarjejeniyar dala biliyan $12.5 baki ɗaya,” inda dala biliyan $7.88 ɗin da Bill ya tura kwanan nan ke matsayin babban ɓangare na wannan kuɗi.
Amfani da Melinda za ta yi da kudin
Sakamakon wannan babban tallafi, gidauniyar Pivotal Philanthropies ta zama ɗaya daga cikin manyan gidauniyoyi masu zaman kansu a Amurka, in ji rahoton jaridar Independent.
Bayanai sun nuna cewa a ƙarshen shekarar 2023, gidauniyar tana da kadarorin dala miliyan $604 kacal, amma zuwa shekarar 2024, kadarorin sun haura zuwa dala biliyan $7.4.
Melinda, tsohuwar matar attajirin duniyar ta riga ta ware dala biliyan $2 daga cikin wannan dukiya don faɗaɗa iko da tasirin mata a fadin duniya.

Source: UGC
Dukiyar da Bill Gate ya mallaka a yanzu
Bill da Melinda sun fara haɗuwa ne a shekarar 1987 kuma suka yi aure a 1994, inda suka haifi ’ya’ya uku: Rory, Phoebe, da Jennifer, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.
Bayan shekaru 27 na aure, sun sanar da rabuwarsu a 2021. A watan Janairun 2025, Bill Gates ya bayyana rabuwar tasu a matsayin “babban abin da na fi nadama” a rayuwata.
Duk da wannan rabuwar, Bill na ci gaba da riƙe matsayin ɗaya daga cikin hamshaƙan attajiran duniya da dukiya ta dala biliyan $118, yayin da Melinda ke da kusan dala biliyan $29.4 sakamakon yarjejeniyar sakin da aka kiyasta darajarta ta kai dala biliyan 86.
Bill Gates zai kyautar da gaba daya dukiyarsa
A wani labari, mun ruwaito cewa, Bill Gates ya sanar da cewa zai ba da kyautar dukiyar sa gaba ɗaya nan da shekara 20, kuma zai rufe gidauniyar BMGF a 2045.
Mai kudin duniya na 13 a lokacin ya yanke shawarar sadaukar da dukiyarsa gaba daya domin ceton rayuka da gina al'umma a duniya.
Bill Gates, wanda ya rasa wani kaso na dukiyarsa bayan ya rabu da matarsa Melinda ya nuna cewa lokaci ya yi da zai kawo karshen ayyukan da ya shafe shekaru yana yi.
Asali: Legit.ng

