Bayan sanar da shirin rabuwa, Bill Gates da Melinda sun tsinke igiyoyin aurensu

Bayan sanar da shirin rabuwa, Bill Gates da Melinda sun tsinke igiyoyin aurensu

  • Alkali ya amince da rabuwar auren hamshakin mai kudi Bill Gates da matarsa Melinda French Gates
  • Dama sun gabatar da takardar bukatar a raba aurensu mai shekaru 27 ne tun ranar 3 ga wata Mayu
  • Saidai ba a tabbatar da rabuwar auren nasu ba sai a ranar Litinin sannan babu wata yarjejeniyar raba dukiya da sukayi

Washington, Amurka - Auren mashahurin mai kudin nan na duniya Bill Gates da matarsa Melinda French Gates ya rabu kamar yadda alkali ya amince da rabuwar tasu, theCable ta wallafa.

Dama sun gabatar da takardar amincewa da rabuwar aurensu mai shekaru 27 tun 3 ga watan Mayu zuwa babbar kotu ta King County dake Washington kuma an tabbatar da rabuwar tasu a ranar Litinin.

Bill da Melinda sun jima suna yada rabuwar aurensu kuma sun amince da yadda zasu raba auren.

Bayan sanar da shirin rabuwa, Bill Gates da Melinda sun tsinke igiyoyin aurensu
Bayan sanar da shirin rabuwa, Bill Gates da Melinda sun tsinke igiyoyin aurensu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Babu yarjejeniyar raba dukiya ko bada wani kaso

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Tsohon sanatan Najeriya ya rasu bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya

Sai dai kamar yadda Reuters suka tabbatar, babu wani dogon bayani akan rabuwar auren sannan babu batun raba kudade, kadarori ko wasu dukiya dake tsakaninsu a rabuwar auren.

Rahoton kotu ya bayyana cewa babu wanda zai canja sunansa cikinsu ko kuma ya samu wani tallafi.

Biyun sun dade suna taimakon jama’a ta gudauniyar Bill and Melinda Foundation.

Melinda zata yi murabus daga shugabancin gidauniyarsu

Duk da sun yarda da cewa zasu cigaba da yiwa gudaniyar aiki tare, akwai wata takarda wacce suka gabatar wa ma’aikatansu wacce TheCable ta ruwaito inda suka ce idan wani daga cikinsu ya ga ba zai iya cigaba da yi musu aiki ba, Melinda za tayi murabus daga shugabancin gidauniyar.

Sun dade suna bayyana cewa zasu cigaba da aiki tare a matsayin shugabannin gudauniyar,” kamar yadda Mark Suzman ya tabbatar, CEO na gidauniyar.
Saidai idan daya daga cikinsu ya yanke shawarar daina aiki da daya, Melinda zata sauka shugabar kungiyar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Hadiman Sunday Igboho, Ta Fadi Dalili

Bill da Melinda sun hadu ne a 1987 kuma sun yi aure a 1994 sannan sun kafa gidauniyarsu a 2000.

Abinda ya hana mu ceto daliban makarantar Tegina, Gwamnatin Neja

Gwamnatin jihar Neja ta bayar da dalilan da zasu iya janyo bacin lokaci wurin ceto yaran makarantar islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina.

Yayin da sakataren jihar, Ahmed Matane, yake tattaunawa da ThisDay a ranar Litinin, ya bayyana yadda iyayen yaran suka dakatar da amfani da sojoji wurin ceto yaran.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta so amfani da sojoji wurin shiga dajin su bude wuta su ceto yaran amma iyayen yaran sun dakatar dasu saboda gudun rasa rayukan yaran garin yin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel