An Yi Rashi: Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Ya Rasu a Saudiyya

An Yi Rashi: Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Ibrahim Tanko Ya Rasu a Saudiyya

  • Tsohon alkalin alkalan Najeriya, Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad, ya rasu a Saudiyya kwanaki kafin cikarsa shekaru 72
  • Kungiyar dalibai ta NAMLAS ta bayyana mutuwar Tanko a matsayin babban rashi ga bangaren shari’a, Musulmi da Najeriya baki daya
  • An yaba da irin gaskiya, tawali’u da rawar da marigayin ya taka wajen jagorantar matasan lauyoyi Musulmi a fadin kasar Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Saudiyya - Tsohon babban Alkalin Alkalai na Najeriya (CJN), Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad (mai ritaya), ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon CJN din mai shekaru 71 ya rasu a wani asibiti da ke kasar Saudiyya, kimanin makonni biyu kafin cikar sa shekaru 72 a ranar 31 ga Disamba.

Tsohon babban alkalin Najeriya, Justice Ibrahim Tanko ya rasu
Tsohon alkalin alkalan Najeriya, Justice Ibrahim Tanko da ya rasu a Saudiyya. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Alkali Ibrahim Muhammad Tanko ya rasu

Kungiyar dalibai Musulmai masu karantar lauyanci ta Najeriya (NAMLAS) ce ta tabbatar da rasuwar tasa a wata sanarwar ta’aziyya da ta fitar a ranar Talata a Abuja, in ji rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Musulunci ya yi rashi: Shugaban kungiyar Izalah a Gombe, Abdullahi Barde ya rasu

A cikin sanarwar mai taken “Sakon Ta’aziyyar NAMLAS kan Rasuwar Mai Girma Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad, GCON, Tsohon Babban Alkalin Alkalai na Najeriya”, kungiyar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga kasa baki daya.

Sanarwar ta ce:

“Kungiyar dalibai Musulmi masu karantar lauyanci ta Najeriya (NAMLAS), ta samu labarin rasuwar Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad, tsohon Babban Alkalin Alkalai na Najeriya.
"Rasuwarsa babban rashi ne ga bangaren shari’a na Najeriya, harkar lauya, al’ummar Musulmi da kasa baki daya.”

NAMLAS ta bayyana marigayi Mai shari'a Tanko a matsayin babban mutum mai riko da gaskiya, tawali’u da jajircewa wajen tabbatar da adalci.

An yaba wa mariyagi Justice Ibrahim Tanko

A cewar kungiyar, a tsawon rayuwarsa ta aikin shari’a, ya kasance abin koyi wajen adalci, jarumtaka da rikon amana ga doka.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Yayin da yake rike da mukamin alkalin alkalai na Najeriya, ya gudanar da aikinsa cikin hikima da kamun kai, inda ya bar abin koyi da zai ci gaba da zama jagora ga al’ummar lauyoyi."

Kara karanta wannan

"Ba zan taba komawa APC ba," Sanata ya yi kaca kaca da gwamnoni 6 a Najeriya

Kungiyar ta kuma yaba da rawar da marigayin ya taka wajen jagoranta da tallafa wa dalibai Musulmi masu karantar lauyanci a fadin kasar, in ji rahoton SaharaReporters.

“Ga NAMLAS, tsohon alkalin alkalan bai kasance alkali kawai ba, ya kasance uba, ginshiki da kuma tushen kwarin gwiwa ga dalibai Musulmi masu karantar lauyanci a fadin Najeriya,” in ji kungiyar.
Dalibai lauyoyi sun yi ta'aziyyar Justice Ibrahim Tanko
Ibrahim Tanko ya na karanta rantsuwar kama aiki. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Dalibai lauyoyi sun yi ta'aziyyar Tanko

An kara da cewa goyon baya, shawarwari da bude kofar sauraron burin matasan lauyoyi da ya yi, na nuna irin yadda ya yi imani da tarbiyya da gina shugabannin shari’a na gaba.

Kungiyar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, bangaren shari’a na Najeriya, gwamnati da al’ummar Musulmi baki daya.

“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa, bangaren shari’a na Najeriya, gwamnati da al’ummar Najeriya, da kuma daukacin al’ummar Musulmi.”

NAMLAS ta kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, kuma Ya ba shi Aljannar Firdausi.

'Ya 'yan Tanko sun samu tikitin takara

A wani labari, Legit Hausa ta rahoto a 2021 cewa 'ya'ya biyu na Mai shari'a Ibrahim Tanko, sun samu tikitin takarar kujerun majalisar tarayya a zaben 2023 a Bauchi.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankar kauna: An tabbatar da rasuwar tsohon jagora a NLC ta kasa

Wani daga cikin 'ya'yan, Siraj Ibrahim Tanko, ya samu nasarar caraf da tikitin takarar sanata a karkashin jam'iyyar APC domin wakiltar mazabar Bauchi ta Arewa.

'Dayan 'dan CJN, Sani Ibrahim Tanko, ya yi nasara ne a jam'iyyar PDP a mazabar Shirya Giafe inda zai wakilce su a majalisar wakilai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com