Muhimman abubuwa 7 a kan sabon Alkalin Alkalai, Ibrahim Tanko

Muhimman abubuwa 7 a kan sabon Alkalin Alkalai, Ibrahim Tanko

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Justice Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin mukadashin Alkalin Alkalai na Najeriya.

Wannan ya biyo bayan dakatar da tsohon Alkalin Alkalai Walter Onnoghen ne da shugaban kasar ya yi a ranar Juma'a bisa umurnin kotun da'ar ma'aikata CCT.

Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman abubuwa da ya dace ku sani a kan Justice Muhammad kamar yadda muka samu daga shafinsa na tattara bayanai na Wikipedia.

Muhimman abubuwa 7 da ya dace ka sani a kan sabon Alkalin Alkalai, Ibrahim Tanko
Muhimman abubuwa 7 da ya dace ka sani a kan sabon Alkalin Alkalai, Ibrahim Tanko
Asali: Facebook

1. An haifi Justice Muhammad ne a ranar 31 ga watan Disambar 1953 a karamar hukumar Doguwa-Giade da ke jihar Bauchi

2. Ya yi karatu a makarantar sakandare na Azare inda ya samu takardan WAEC a 1973 kafin ya wuce zuwa jami'an Ahmadu da ke Zaria inda ya kammala karatun digiri a fanin Shari'a a 1980.

3. Daga bisani ya yi digiri na biyu (Msc) da digiri na uku (PhD) duk a jami'an Ahmadu Bello da ke Zaria a 1984 da 1998.

4. An nada shi a matsayin lauya a 1981 sannan ya fara aiki a shekarar 1981.

DUBA WANNAN: Jigo a jam'iyyar APC ya fadi su waye ke tsoron tazarcen Buhari

Wannan ya biyo bayan dakatar da tsohon Alkalin Alkalai Walter Onnoghen ne da shugaban kasar ya yi a ranar Juma'a bisa umurnin kotun da'ar ma'aikata CCT.

Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman abubuwa da ya dace ku sani a kan Justice Muhammad kamar yadda muka samu daga shafinsa na tattara bayanai na Wikipedia.

1. An haifi Justice Muhammad ne a ranar 31 ga watan Disambar 1953 a karamar

5. A 1989, an nada shi babban kotun majistare na babban birnin tarayya Abuja inda ya yi aiki har zuwa lokacin da aka nada shi Alkali a Kotun Shari'a na daukaka kara da ke Bauchi.

6. Ya cigaba da aiki a matsayin Alkali a Bauchi na tsawon shekaru 13 sannan aka nada shi Alkali a Kotun Koli ta kasa a 2006 amma ya fara aiki a ranar 7 ga Janairun 2007.

7. A ranar 25 ga watan Janairun 2019, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi mukadashin Alkalin Alkalai bayan dakatar da Justice Walter Onnoghen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel