Nijar da Wasu Kasashen Afrika 5 da Amurka Ke da Sansanin Sojoji a cikinsu

Nijar da Wasu Kasashen Afrika 5 da Amurka Ke da Sansanin Sojoji a cikinsu

Tun bayan da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, al’umma ke ci gaba da fargabar irin matakin da zai iya ɗauka.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa zai ɗauki matakin soja ne idan hukumomin Najeriya suka kasa dakatar da abin da ya kira “kisan Kiristoci” a ƙasar.

Akwai kasashen Afrika 5 da Amurka ke da sansanoni a cikinsu
Sojojin Amurka a sansaninsu na Niamey, Jamhuriyyar Nijar. Hoto: @africa_intel
Source: Twitter

China ta yi martani ga kalaman Trump

Wannan furuci na Trump ya tayar da jijiyoyin wuya a Najeriya da wajen ƙasar, kamar yadda China ta yi gargadi a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 4 ga watan Nuwamba, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin tsaron China, Mao Ning ta ce tana tare da Najeriya a wannan lamari.

Mao Ning ta kuma bayyana cewa:

"Muna adawa da duk wata kasa da za ta tsoma baki a harkokin wata kasar da sunan addini ko 'yancin kai. Muna adawa da barazanar Trump ta janye tallafi ko daukar matakin soja kan Najeriya."

Kara karanta wannan

Sakon Tinubu ga 'yan Najeriya a kan barazanar Donald Trump

Masana harkokin tsaro da diflomasiyya sun yi gargadi cewa wannan tsoma bakin na iya janyo rikici ko tabarbarewar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

Wasu masana sun bayyana cewa, kodayake Trump ya yi nufin kare Kiristoci, amma matakin na iya zama babban kalubale ga ikon ƙasa da zaman lafiya a Najeriya, musamman idan Amurka ta ɗauki matakin soja.

Yadda Amurka za ta iya kai hari Najeriya

A cewar masana harkokin tsaro, Amurka — wadda ita ce ƙasa mafi ƙarfin soja a duniya — na iya ɗaukar matakin soji a hanyoyi biyu, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Na farko, ta hanyar kai farmaki kai tsaye kan ƙungiyoyin da ake zargin suna da hannu wajen kashe Kiristoci da Musulmi masu ra’ayin zaman lafiya.

Wannan zai iya haɗawa da kai hare-haren jiragen sama, da kuma amfani da sojoji na musamman domin kakkaɓe sansanonin ƙungiyoyin da ake zargi kamar Boko Haram da ISWAP.

Yawanci irin wannan nau’in farmakin ana gudanar da shi ne cikin sauri tare da nufin kawo ƙarshen barazana a lokaci guda.

Kara karanta wannan

"Najeriya ba ta da damar goyon bayan kisan addini": Minista ya karyata Trump a idon duniya

Hanyar ta biyu kuma ita ce kafa sansanonin soji a cikin Najeriya, inda Amurka za ta dinga tattara bayanan sirri da horar da jami’an tsaro.

Wannan hanya tana ba Amurka damar kasancewa a yankin na tsawon lokaci domin gudanar da bincike da kuma dakile hare-hare.

Ƙasashen Afirka da Amurka ke da sansanonin sojoji

Masana sun ce, tuni Amurka ke da sansanonin soji a akalla ƙasashe huɗu a nahiyar Afirka, waɗanda take amfani da su wajen horar da jami’ai, tattara bayanan leƙen asiri, da kuma yaƙar ta’addanci.

Ga wasu daga cikinsu:

1. Djibouti — Camp Lemonnier:

Djibouti ne sansanin Amurka a yankin Horn of Africa.
Hoton sansanin sojojin Amurka da ke Djibouti, a yankin Horn of Africa. Hoto: @africa_intel
Source: Twitter

Wannan shi ne sansanin soja mafi girma da Amurka ke da shi a nahiyar Afirka, wanda yake a yankin Horn of Africa, da ake kuma kira Somali Peninsula.

Amurka ta karbi hayar sansanin daga Faransawa a 2002, kuma a 2014 ta sabunta yarjejeniyar hayarsa na shekaru 20 akan kuɗin shekara-shekara na dala miliyan 63.

Sansanin na dauke da manyan kayan aiki, jiragen leken asiri da suke taimaka wa wajen ayyukan yaƙi da ta’addanci a yankin Gabas ta Afirka da Tekun Arabiya.

Kara karanta wannan

China ta nunawa Trump yatsa, ta gargadi Amurka kan barazana ga Najeriya

2. Kenya — Manda Bay:

Sansanin Manda Bay na bakin teku yana aiki tun 2006, inda ake gudanar da horo da ayyukan ceto da kuma sintiri a yankin Gabas ta Afirka, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A 2020, mayakan al-Shabab suka kai farmaki a sansanin, inda sojojin Amurka uku suka mutu. Duk da haka, ayyuka sun ci gaba a sansanin tare da haɗin gwiwar sojojin Kenya.

3. Nijar — Air Base 101 da Air Base 201

A Nijar, Amurka na da sansanonin soji biyu; daya a Niamey (Air Base 101) da kuma dayan a birnin Agadez, watau Air Base 201.

Sansanonin nan biyu suna ba Amurka damar gudanar da ayyukan jiragen leƙen asiri da dabarun ISR, domin yaki da ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya a yankin Sahel.

Duk da haka, bayan rikicin diflomasiyya a 2024, gwamnati ta Nijar ta bukaci sojojin Amurka su bar ƙasar.

4. Masar — MFO South Camp (Sinai):

Kara karanta wannan

"Zan goyi bayan Trump": Wike ya yi magana kan barazanar shugaban Amurka

Masar — MFO South Camp (Sinai) - Sansanin sojin Amurka
Hoton sansanin sojojin Amurka na Masar — MFO South Camp (Sinai). Hoto: @africa_intel
Source: Twitter

Amurka tana da dakarunta a ƙarƙashin shirin dakarun yaki da sanya ido na hadin gwiwa na kasa da kasa (MFO) don tabbatar da zaman lafiya tsakanin Masar da Isra’ila bisa yarjejeniyar 1979.

Haka kuma, Amurka na da cibiyar bincike ta NAMRU a Alkahira don bincike tare da ganowa gami da yaki da cututtukan da ke yaɗuwa.

5. Kamaru — Garoua:

A sansanin Garoua ne Amurka ke gudanar da ayyuka tare da dakarun Kamaru domin yaƙi da Boko Haram da ISIS a Yammacin Afrika.

Sojojin Amurka suna ba da horo, samar da bayanan sirri, da tallafin fasaha don tabbatar da tsaron yankin Tafkin Chadi.

Wannan haɗin gwiwa yana zama muhimmin bangare na yunkurin Amurka wajen tallafawa yaki da ta’addanci a yankin Afrika ta Yamma, inda ya shafi Najeriya kai tsaye.

Amurka za ta kafa sansanin sojoji a Najeriya?

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya karyata zargin cewa kasashen waje za su kafa sansanonin sojojinsu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zargin kisan kiristoci: Wike ya zargi 'yan adawa da wuce gona da iri wurin yada karya

Mohammed Idris, a cikin wata sanarwar da ya fitar ya ce labarin da ake yadawa kan kafa sansanonin Amurka da Faransa karya ce kwai aka shirya.

Ministan yada labaran ya kuma jaddada cewa Najeriya ta riga ta samu duk wani taimako daga kasashen waje da take bukata wajen samar da tsaro da kanta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com