Amurka zata janye daga Afghanistan, bayan sulhu da Taliban da ta yaka tun 2001

Amurka zata janye daga Afghanistan, bayan sulhu da Taliban da ta yaka tun 2001

- Amurka zata janye daga Afghanistan

- Shekaru 17 tana yaki a kasar

- An fara jihadi a Afghanistan tun 1970s

Amurka zata janye daga Afghanistan, bayan sulhu da Taliban da ta yaka tun 2001
Amurka zata janye daga Afghanistan, bayan sulhu da Taliban da ta yaka tun 2001
Asali: Getty Images

Amurka tace zata janye fin rabin sojojinta daga kasar Aghanistan, kasar da ake ta yaki tun 1970, lokacin da kasar Rasha ta fada wa kasar.

Akwai sojin Amurka 7,000 a kasar, wadanda ke agazawa na kasar da Atisaye, koyarwa da goyon baya kan tsaro a kasar mai dumbin tarihi wadda yaki ya mayar qauye shekaru kusan 50.

Mujahidan Taliban dai sun kwace gwamnatin, tun a 1980s, inda suka dabbaka shari'ar Islama suka kori ilimin Boko da zamananci, saboda komawa 'tafiyar Salaf ta magabata', kamar dai yadda Boko Haram ke kwaikwayo yanzu haka a Najeriya.

Wannan ya bada dama masu kokarin maye duniya da addinin Musulunci suka kafa sansanoninsu a kasar, kungiyar Alqaida ta Bin-Laden itace ta kai hari Amurka a 2001, wadda hakan yasa Amurkar ta kai hari ta kori Taliban din daga birane.

DUBA WANNAN: Assha! Gasar inzali ta kai wani jarumin mata lahira, a zagaye na bakwai

Sai dai maimakon su hakura, Taliban sun koma yakin sunquru inda suke dana Bam a sansanonin soji,m 'yansanda, makarantu, da ma kashe dalibai masu karatun boko, musamman mata.

An dai kira Taliban sulhu kasar Oman, da kasar Qatar, a lokuta da dama, inda ake basu mayakansu da aka kulle a Guantanamo dake Cuba, su kuma su saukaka muguntarsu kan 'yan kasarsu da suke kashe wa.

A wannan karon, an roke su dasu ajje makamai, su zamo jam'iya mai neman quri'u, in sunci zabe sai su kawo shari'a a yankunan da aka zabe su, in sun fadi, sai su hakura su jira zabuka na gaba.

Sojin Amurka dai da yawa sun hallaka a kasar ta Afghanistan, a koakrinsu na kakkabe burbushin Taliban da Al-Qaida, sai dai shugaban Amurka Trump, yace zai kawo karshen yakin wanda ya lakume rayuka da fin Tiriliyann daya ta dalolin Amurka.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel