Asrani: Fitaccen Jarumin Barkwanci a Fina Finan Indiya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Asrani: Fitaccen Jarumin Barkwanci a Fina Finan Indiya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Fitaccen jarumin barkwanci a fina finan Bollywood, Govardhan Asrani, ya rasu yana da shekara 84
  • Govardhan Asrani ya taka rawar “gandiroba” a fim din Sholay (1975), wanda ya haska tauraruwarsa
  • An birne shi cikin sirri kamar yadda ya bukata, yayin da masana’antar Bollywood ke alhinin rasuwarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Indiya - Fitaccen jarumin fina-finan Bollywood, Govardhan Asrani, ya rasu a ranar Litinin da rana bayan fama da matsalar numfashi.

Jarumin mai shekaru 84 ya rasu ne a Asibitin Bharatiya Arogya Nidhi da ke Juhu, Mumbai, inda aka kwantar da shi bayan likitoci sun gano taruwar ruwa a cikin huhunsa.

Fitaccen jarumin barkwancin Indiya, Asrani ya rasu yana da shekaru 84
Hoton jarumi Asrani ya goya Akshay Khumar a babur a cikin wani fim, da hotonsa shi kadai. Hoto: @upuknews1
Source: Twitter

Jarumin Bollywood, Asrani ya rasu

Jaridar Indian Times ta rahoto cewa, manajansa, Babubhai Thiba, ya tabbatar da rasuwarsa ga manema labarai, yana mai cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“An shigar da shi (Govardhan Asrani) asibiti bayan ya fara samun matsalar numfashi. Daga baya likitoci suka ce ruwa ya taru a huhunsa. Ya rasu da misalin karfe 3:00 na rana.”

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a jam'iyyar hadaka, an dakatar da mataimakin shugaban ADC na kasa

An gudanar da jana’izarsa a makabartar Santacruz da yammacin ranar Litinin, inda danginsa da abokansa na kusa suka halarta cikin sirri, kamar yadda ya bar wasiyya.

Asrani ya kafa tarihi a Bollywood

Asrani ya shahara saboda rawar da ya taka a fim din Sholay (1975) inda ya fito a matsayin jami’in gidan yari mai ban dariya.

Kalaman da ya fi furtawa “Hum angrezon ke zamane ke jailor hain (Mu masu zaman kurkuku ne daga lokacin Burtaniya)” suka zama abin tunawa a duniyar fina-finai har yanzu.

Rawar da ya taka a wannan fim din ta kara masa daukaka a matsayin jarumin barkwanci da azancin magana ba ya kare masa yayin da yake magana.

Masana sun kwatanta salon sa da na Charlie Chaplin a fim din The Great Dictator.

Rayuwar Asrani da nasarori a fim

Asrani ya fara sana’ar fim a shekarun 1960, bayan ya kammala karatu a cibiyar koyar da fim da aikin talabijin ta Indiya (FTII), da ke Pune.

A cikin shekaru fiye da 50, ya fito a fim sama da 300, ciki har da Guddi, Namak Haram, Bawarchi, Hera Pheri, Hulchul, da Welcome.

Kara karanta wannan

Yadda gwamna Abba ya sa baki a rikicin dan jarida da hadiminsa a Kano

Ya yi aiki tare da fitattun jarumai kamar Amitabh Bachchan, Rajesh Khanna, Akshay Kumar da Paresh Rawal, abin da ya nuna yadda barkwancinsa ya dace da kowane zamani na Bollywood.

Duk da shahararsa a barkwanci, Asrani ya kuma taka rawar gani a fina-finai masu cike da natsuwa kamar Aaj Ki Taaza Khabar da Chala Murari Hero Banne, wanda shi da kansa ya bada umarni.

Fitaccen jarumin barkwancin Indiya, Asrani, ya rasu
Hotunan fitaccen jarumin barkwancin Indiya, Asrani da ya rasu. Hoto: @Dev_Fadnavis
Source: Twitter

An yi jana'izar jarumin Bollywood a sirrance

A cewar manajansa, Asrani ya bukaci a binne shi cikin sirri, ba tare da sanar da jama’a ba, in ji rahoton Hindustan Times.

“Ba mu iya sanar da mutuwarsa ba a lokacin da ya rasu, saboda ya bar mana wasiyya cewa kada a yi hayaniya ko nadar bidiyon jana'izarsa,” in ji Thiba.

Asrani ya mutu ya bar matarsa da ‘ya’ya, kuma Indiyawa za su ci gaba da tunawa da son jama'a da kalaman barkwancinsa.

Jarumin Bollywood, Rishi Kapoor ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitaccen jarumin Bollywood, Rishi Kapoor ya riga mu gidan gaisuwa bayan shekaru yana jinya.

A cikin wata sanarwa, jarumin masana'antar, Amitabh Bachchan ya bayyana cewa mutuwar Rishi Kapoor ta matukar girgiza shi.

Kara karanta wannan

'Yar ƙwaya ce fa yanzu': Sanata ya ƙaryata zargin cin zarafin matarsa a gidan aure

Rishi Kapoor ya rasu ne a asibitin Sir HN Reliance Foundation da ke birnin Mumbai yayin da yake da shekaru 76 a duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com