Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana

Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana

- Arzikin da harkar fim ke kawowa yana da yawa sosai a kasar Indiya

- An kusa shekara 80 ana harkar fim a kasar mai dumbin tarihi

- Fina-finnansu sun sami karbuwa a Asiya da Afirka, amma banda Turai

Fim din October: Labari ne kan soyayya wanda aka sake shi a ranar 13 ga watan Afrilun 2018. Shoojit Sircar ne ya bayar da umarninsa.

Varun Dhawan da sabuwar yarinya Banita Sandhu suka fito a ciki. Labari ne na Dan (Varun Dhawan) da ke tafiyar da rayuwarsa kamar kowane matashi dan shekara 21 .

Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana
Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana

Padmavati: Tarihi ne na soyayya da ya taba faruwa tsakanin wani sarki musulmi da wata gimbiya mai bin addinin Hindu, kamar dai yadda aka tsara Jodha Akbar a baya a 2008.

Fim din an kashe masa makudan kudade, kuma ya tara akalla dala $90m tun daga sakinsa a watan Yanairun bana ya zuwa yanzu.

Sai dai lokacin da aka saki fim din an sami tarnaqi daga masu zazzafan kishin addinin Hindu wadanda suke ganin fim din bai kama da yadda tarihin yake ba.

Musamman ganin jarumar, (Deepika Padukone), har kone kanta tayi a cikin shirin duk don kar sarkin musulmin ya kama ta ko ya ci garinta da yaki.

An dakatar da sakin fim din na wani dan lokaci, bayan da wasu suka saki sanarwar zasu kashe aftawan fim din dama daraktocin fim din.

Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana
Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana

Baaghi 2: Tiger Shroff, da ga Jackie Shroff shi ya fito a wannan zazzafan fim da aka qaga labarinsa domin nishadin Indiyawa da masu kallon fim.

Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana
Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana

DUBA WANNAN: Mun daina Sulhu da Boko Haram

Pad Man:

An saki Fim din Pad Man a ranar 9 ga watan Fabrairun 2018. Fim ne wanda Twinkle Khanna ta shirya shi, R. Balki kuma ya bayar da umarninsa.

Fim ne da ya kunshi barkwanci kuma an yi shi ne da nufin wayar da kan mutane a kan su dai na kyamatar mata idan suna jinin al'ada.

Akshay Kumar ne afto a fim din kuma baya ga barkwanci, akwai darussa sosai a im din, musamman bibiyar yadda al'adun Indiya suke na rashin wayewa.

Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana
Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana

Hitchki:

Fim ne wanda Maneesh Sharma ya shiya shi, Sidharth P Malhotra kuma ya bayar da umarninsa. An sake shi a ranar 23 ga watan Maris na bana. Jaruma Rani Mukherjee ce ta fito a cikin fim din.

Fim din ya kunshi labarin wata mata mai fama da larurar Tourette's (wata larura da kan shafi laka wadda alamominta su ne motsin wasu sassan jiki da fitar sauti ba da niyya ba).

Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana
Mu leka Bollywood: Fina-finan Indiya da suka fi qayatar wa a bana

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel