Wani shahararren jarumin Bollywood ya sake rasuwa

Wani shahararren jarumin Bollywood ya sake rasuwa

Bayan kwana daya tak da rasuwar fitaccen jarumin Bollywood, Irrfan Khan, mun samu labarain mutuwar jarumi Rishi Kapoor.

Rishi Kapoor ya kwashe shekaru biyu cif yana jinyar cutar kansa.

Fitaccen jarumi Rishi Kapoor ya rasu ne a asibitin Sir HN Reliance Foundation da ke birnin Mumbai.

Ya rasu a kasar Indiyan ne a yayin da yake da shekaru 76 a duniya kamar yadda BBC ta ruwaito.

Neetu Kapoor ce matarsa wacce ta shafe tsawon lokaci tana jinyarsa kafin rasuwarsa.

Dan uwansa mai suna Randhir Kapoor ne ya sanar da rasuwar marigayin.

Fitaccen jarumin masana'antar, Amitabh Bachchan ya sanar da cewa mutuwar ta matukar girgiza shi a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter.

Kamar yadda ya wallafa, "Rishi Kapoor... ya tafi... ya yi gaba... Na halaka!"

A shekarar 2018, marigayi Rishi Kapoor ya kamu da cutar kansa wanda hakan yasa ya kwashe fiye da shekara daya a birnin New York yana karbar magani.

Bayan murmurewarsa, ya dawo kasar Indiya a watan Satumban 2019.

Rishi da ne ga marigayi Raj Kapoor. A cikin 'yan uwansa akwai Randhir, Riti Nanda, Rima Jain da kuma Rajeev Kapoor.

Wani shahararren jarumin Bollywood ya sake rasuwa
Wani shahararren jarumin Bollywood ya sake rasuwa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa mahaifiyar Gwamna Fintiri rasuwa

An fara haska jarumin a fim dinsa na farko ne mai suna Bobby wanda ya yi tare da Dimple Kapadia a 1973.

Ya bayyana ne a matsayin mai wasan kwaikwayon yara a fina-finai kamar su Shree 420 da Mer Naam Joker.

Ya bayyana a fina-finai masu farin jini irinsu Amar Akbar Anthony, Laila Majnu, Rafoo Chakkar, Sargam, Karz, Bol Radha Bol da sauransu.

Ya fito a manyan fina-finai irinsu Kapoor and Sons, D-Day, Mulk da 102 Not Out.

A wani labari na daban, mun ji cewa Allah ya yi wa Hajiya Fatimah Umar Badami, mahaifiyar gwamnan jihar Adamawa rasuwa.

Mahaifiyar Gwamna Ahmadu Fintiri ta rasu ne tana da shekaru 68 a duniya.

Hajiya Fatimah Badami ta rasu ne a yau Laraba a asibitin tarayya da ke Yola bayan gajeriyar rashin lafiyar da ta yi, kamar yadda takarda daga gidan gwamnatin jihar Adamawa ta bayyana.

Takardar ta fito ne daga daraktan yada labarai da sadarwa na gidan gwamnatin, Solomon Kumangar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel