Wata Sabuwa: 'Yan Sanda Sun Cafke Tsohon Shugaban Kasa kan Zargin Rashawa a Sri Lanka

Wata Sabuwa: 'Yan Sanda Sun Cafke Tsohon Shugaban Kasa kan Zargin Rashawa a Sri Lanka

  • An cafke tsohon shugaban ƙasar Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe bisa zargin amfani da dukiyar gwamnati ba bisa ka'ida ba
  • An kama Wickremesinghe ne bayan bincike kan ziyarar da ya kai wata jami'ar London, inda ya halarci bikin karrama matarsa
  • A yau, 22 ga Agusta, 2025, aka ga mambobin jam’iyyarsa ta UNP suna isa kotun Colombo Fort domin halartar zaman shari’arsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sri Lanka - ’Yan sandan Sri Lanka sun cafke tsohon shugaban ƙasar, Ranil Wickremesinghe, a ranar Juma’a, 22 ga Agusta, 2025, bisa zargin rashawa.

Wikcremesinghe ya zama fitaccen ɗan adawa mafi girma da aka tsare ƙarƙashin shirin yaƙi da cin hanci da rashawa na sabuwar gwamnatin Sri Lanka.

Jami'an 'yan sanda sun kama tsohon shugaban Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe kan zargin rashawa
Tsohon shugaban Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe a filin taron kaddamar da jami'an rundunar sojin sama na kasar. Hoto: @RW_SRILANKA
Source: Twitter

An kama tsohon shugaban kasar Sri Lanka

Rahoton Reuters ya nuna cewa 'yan sandan sashen CID ne suka kama Wikcremesinghe bisa zargin yin amfani da kuɗaɗen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi: Sojoji sun damƙe hatsabibin ɗan bindiga, yaransa 13

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CID da hadin gwiwar rundunar yaƙi da cin hanci ta Sri Lanka sun fara wannan aiki ne tun bayan da Shugaba Anura Kumara Dissanayake ya hau mulki a Satumbar 2024.

An tsare Wickremesinghe, mai shekaru 76, bayan bincike kan wata ziyara da ya kai London a Satumbar 2023 domin halartar bikin karrama matarsa a jami’ar Birtaniya.

Wata majiya daga rundunar ‘yan sanda ta Sri Lanka ta tabbatar da cewa, za a gurfanar da tsohon shugaban kasar da ya fadi zaben 2024 a gaban kotun Colombo Fort.

Majiyar ta ƙara da cewa za a a tuhumi Wickremesinghe da laifin amfani da dukiyar gwamnati wajen biyan bukatun kansa.

Zargin da ake yi wa tsohon shugaban kasar

A shekarar 2023, aka rahoto cewa ya tsaya a London a hanyarsa ta dawowa daga Havana inda ya halarci taron kolin ƙungiyar G-77.

An ce tsohon shugaban kasar da matarsa Maithree sun halarci bikin jami’ar Wolverhampton, inda aka karrama ta da matsayin 'farfesar girmamawa'.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu

Wickremesinghe ya dage cewa matarsa ce ta biya kudin wannan tafiyar, don haka babu wasu kuɗin gwamnati da aka yi amfani da su.

Amma hukumar yaki da laifuffukan ta'addanci ta kasar ta dage cewa shi da hadimansa sun yi amfani da kuɗin gwamnati a tafiyar da suka yi ba a hukumance ba.

A ranar Juma’a, aka ga mambobin jam’iyyarsa ta UNP suna isa kotun Colombo Fort domin halartar zaman shari’arsa, inji rahoton Yahoo News.

Ranil Wickremesinghe ya hau kan mulkin kasar Sri Lanka domin karasa wa'adin Gotabaya Rajapaksa da ya yi murabus.
Tsohon shugaban kasar Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, a lokacin yakin neman zabensa a 2024. Hoto: @RW_SRILANKA
Source: Twitter

Wa'adin Wickremesinghe a mulkin Sri Lanka

Wickremesinghe ya hau mulki a watan Yulin 2022 domin kammala wa’adin Gotabaya Rajapaksa, bayan da Rajapaksa ya yi murabus sakamakon zanga-zangar da aka gudanar kan zargin rashawa da gazawar mulki.

Ya samu tallafin bashi na dala biliyan 2.9 daga asusun IMF a farkon 2023, abin da ya taimaka wajen daidaita tattalin arziƙi bayan tabarbarewar kudi mafi muni a tarihin kasar a 2022.

A matsayin matakan tsauraran tattalin arziki, ya ninka haraji sau biyu tare da cire tallafin makamashi domin ƙara samun kuɗin shiga ga gwamnati.

Masu zanga-zanga a fadar shugaban kasa

Kara karanta wannan

Nijar: An harbe shugaban Boko Haram da ya maye gurbin Shekau har lahira

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dubban masu zanga-zanga a Sri Lanka sun mamaye gidan fadar shugabankasa a Colombo don neman yayi murabus.

Hotuna sun nuna masu zanga-zangar sun kutsa har cikin ɗakin kwanan shugaban kasar inda suka rinƙa ɗaukar hotuna a kan gadonsa da zama kan kujeru.

Mutanen kasar Sri-Lanka sun kwashe shekaru goma suna fama da matsin tattalin arziki wanda ya sa suka nemi Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya yi murabus.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com