Gwamnatin kasar Sri Lanka ta haramta sanya Niqabi da kulle Islamiyyu sama da 1,000

Gwamnatin kasar Sri Lanka ta haramta sanya Niqabi da kulle Islamiyyu sama da 1,000

- Kasar Sri Lanka mai karancin mabiya addinin Islama ta soke sanya kayan addini ga Musulmai

- Wannan ya biyo bayan harin kunar bakin wake da aka kai ranar Easter Sunday shekarar 2019

- Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne don tabbatar da tsaro

Gwamnatin kasar Sri Lanka na shirin haramta sanya Niqabi a fadin kasar tare da kulle makarantun Isamiyya akalla 1000 saboda dalili na tsaro.

Ministan tsaron jama'a, Sarath Weerasekera, ya bayyanawa manema labarai ranar Asabar cewa ya rattafa hannu kan wata takarda ranar Juma'a domin majalisar ministoci su amince da haramta sanya Niqabi don tabbatar da tsaro, rahoton Aljzeera.

"A lokacin da muke yara, mata Musulmai da yara basu sanya Niqabi," cewar sa.

"Wannan wani tsattsaurin ra'ayin addini ne da aka kirkiro kwanan nan. Ko shakka babu zamu haramta."

KU DUBA: Daga cikin yan majalisan dokokin tarayya 469, 19 kadai ne mata, ga jerinsu

Gwamnatin kasar Sri Lanka na shirin haramta sanya Niqabi da kulle Islamiyyu sama da 1,000
Gwamnatin kasar Sri Lanka na shirin haramta sanya Niqabi da kulle Islamiyyu sama da 1,000
Source: Twitter

KU DUBA: Mun nemi kudin makaman da muka baiwa su Buratai mun rasa, NSA Monguno yayi fallasa

Weerasekera ya kara da cewa gwamnatin jihar na shirin kulle makarantun Islamiyyu sama da 1000 saboda suna saba dokokin bayar da ilimi a kasar.

"Babu wanda zai bude makaranta yana koyar da yara abinda yake so," yace.

Wannan mataki da gwamnatin ke dauka kan Musulmai ya biyo bayan dokar da ta wajabta na kona gawawwakin wadanda suka mutu sakamakon cutar COVID-19 - wanda Musulmai suka nuna rashin amincewarsu da haka.

Daga baya gwamnatin ta saduda a shekarar nan bayan shan suka daga kasar Amurka da kungiyoyin fafutuka.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel