Tirkashi: An Yi Gwanjon Tsohuwar Safa da Michael Jackson Ya Sanya a 1997 kan N12m
- A wani sabon gwanjon kayan fitaccen mawaki, marigayi Michael Jackson, an sayar da wata safa da ya sanya kan Euro 6,200 a Faransa
- Wani ma'aikaci ne ya tsinci safar a dakin sauya kayan Michael bayan wasan da mawakin ya yi a birnin Nimes na Faransa a Yulin 1997
- Safar ta yi datti kuma ta fara tsufa, amma aka sayar da ita sama da Naira miliyan 12, yayin da aka yi gwanjon wasu kayansa kan $420,000
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Faransa - An yi gwanjon wata safa da aka kawata da lu’u-lu’u wadda Michael Jackson ya sanya yayin wani wasa da ya yi a shekarar 1997 a birnin Nice na kasar Faransa.
An rahoto cewa an sayar da safar kafar fitaccen mawakin ne a kan Euro 6,000, kimanin dala 8,000 ko kuma Naira miliyan 12.2 a farashin canjin yau.

Source: Getty Images
Yadda aka yi gwanjon safar Michael Jackson
An bayyana safar a matsayin "abin kauna ga masoya", kuma tana daga cikin wasu kayan tarihi da aka sayar, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce wani ma'aikaci ne ya tsinci safar a yashe a kusa da dakin da Jackson ke canja kaya bayan an kammala wasan da ya yi a birnin Nimes da ke kudancin Faransa a watan Yuli 1997.
Michael Jackson, wanda ake kira da "Sarkin Pop", ya yi amfani da farar safa da aka kawata da dutsen lu’u-lu’u a lokacin da ya yi zagayen "HIStory World Tour" a 1997.
Ana iya ganin Michael Jackson sanye da safar a cikin bidiyon wasanninsa, musamman lokacin da yake rera wakar "Billie Jean".
Darajar safar Michael Jackson ta kai $8,000
Bayan shekaru, safar, wadda launinta ya sauya zuwa ruwan ƙasa, ta yi datti kuma lu’u-lu’un da ke jikinta ya fara canza launi saboda tsufa, kamar yadda aka nuna a wani hoto da aka wallafa a yanar gizo.
The Business Times ta rahoto wanda ya yi gwanjon kayan Michael Jackson, Aurore Illy ya bayyana cewa:
“Wannan safa ce ta musamman – har ma za ta iya zama abin bauta ga masoya Michael Jackson."
Da farko, an yi kiyasin cewa safar zata kai tsakanin €3,000 zuwa €4,000 ($3,400-4,500), amma a karshe aka sayar da ita kan $8,000 a gidan sayar da kaya na Nimes.
Wasu kadarorin Michael da aka sayar
Wani gidan caca a Macau ya sayi safar hannu mai kyalli da Michael Jackson ya sa a karon farko da ya yi rawar “moonwalk” a 1983 kan $350,000 a 2009.
An ce ana sayar da wannan safar hannun da Jackson ya sa yayin wakar Billie Jean a 1983 a kan $420,000.
Kamfanin da ke kula da ayyukan Michael Jakson wato MJJ ne ya fara bayar da safar hannun tare da wani kwali kyauta ga UNICEF a 1998.
A 2023 kuma, an sayar da wata hula da Michael Jackson ya sanya kafin wani wasa da ya yi a kan sama da $80,000 a birnin Paris.

Source: Getty Images
Mutuwar Michael Jackson a Yunin 2009
A ranar 25 ga Yuni, 2009, fitaccen mawakin Amurka, Michael Jackson, ya rasu sakamakon shakar maganin propofol mai karfi a birnin Los Angeles, California, yana da shekara 50.
Likitan sa na sirri, Conrad Murray, ya ce ya same shi a kwance a kan gado, a gidansa da ke North Carolwood Drive, Holmby Hills, ba ya numfashi, a cewar bayani daga WikiPedia.
Likitoci sun ba shi agajin gaggawa a cikin gidan, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa a asibitin Ronald Reagan UCLA da ke Westwood da karfe 2:26 na rana.
A ranar 28 ga Agusta, 2009, hukumar bincike ta Los Angeles ta tabbatar da cewa kashe Michael Jackson aka yi, ba wai mutuwar kawai ba ce.
Ɗan uwan Michael Jackson ya musulunta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Jermaine Jackson, dan uwa ga marigayi Michael Jackosn ya rungumi addinin Islama, kuma ya fadi yadda rayuwarsa ta sauya.

Kara karanta wannan
Hotuna: An ga yadda ambaliyar ruwa ta rusa gidaje a Borno, mutane sun fara hijira
Jermaine yace ya fara sha’awar musulunci ne a lokacin da suka tafi yawon yin wake wake a yankin gabas ta tsakiya tare da kannen shi mata a shekarar 1989.
Ya ce sai bayan da ya musulunta ne ya samu bayani kan hakikanin haihuwar Annabi Isa, wanda ya sa hankalinsa ya kwanta kuma ya kara saduda da addinin.
Asali: Legit.ng


