Tunawa da gwarzon Mawaki Marigayi Micheal Jackson
- Ranar haihuwar Mawaki Micheal Jackson ta zagayo
- Michael Jackson gwani ne wajen harkar rawa da waka
- Marigayin ya rasu ne yana shekara 50 da haihuwa a Duniya
A jiya 29 na wannan Wata ne na Agusta Ranar haihuwar FitaccenMawakin nan Micheal Jackson ta zagayo.
Micheal Jackson wanda yake fitacce ne a harkar rawa da kida da waka ya rasu ne yana dan shekara 50 a Duniya. A zamanin sa babu wanda ya ci ribar waka kamar sa. Asalin sa bakin fata ne wanda daga baya ya sauya fatar jikin sa zuwa fari ja-wur.
KU KARANTA: Tunawa da Firimiya Tafawa Balewa
Micheal Jackson ban da harkar waka ya kuma iya rawa kamar mazari wanda yake da dinbin masoya a fadin Duniya. Bari ta wannan ma, Jackson kwararren Dan gayu ne. Micheal Jackson ya fara saka ne tare da 'Yan uwan sa tun a shekara 1964 daga baya ya ware na kan sa.
Da Micheal Jackson na da rai da yanzu ya cika shekaru 58 a Duniya. Daya daga cikin ‘Ya ‘yan sa ta tuna da Marigayi Mahaifin na ta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Menene abin dubawa wajen fara soyayya
Asali: Legit.ng