'Ɗan uwan Michael Jackson, Jermaine ya musulunta

'Ɗan uwan Michael Jackson, Jermaine ya musulunta

Jermaine Jackson dan uwa ga marigayi shahararren mawaki Michael Jackosn ya bayyana dalilin daya sa ya rungumi addinin Islama da yadda rayuwarsa ta kasance tun bayan daya musulunta.

'Ɗan uwan Michael Jackson, Jermaine ya musulunta
Jermaine Jackson

Jermaine yace ya fara sha’awar musulunci ne a lokacin da suka tafi yawon yin wake wake a yankin gabas ta tsakiya tare da kannen shi mata a shekarar 1989, inda suka hadu da wasu kananan yara masu kirki, yayin da suke tattaunawa da yaran sai yaran suka fada musu su musulmai ne, kuma suna alfahari da hakan, hakan sai yayi matukar daure ma Jermaine kai.

KU KARANTA: Mashawarcin shugaba Buhari ya ɗau alwashin maka Saraki a kotu, me yayi zafi? (Karanta)

Legit.ng ta ruwaito shi yana cewa “Nan fa suka fara wayar min da kai game da musulunci, suna bani bayani daidai na shekarunsu, daga muryarsu zaka gane lallai suna alfahari da addininsu. Daga nan ne na fara sha’awar musulunci. Kaji yadda hira da kanana yara ya kai nig a musulunci, har na fara tattauna batun da manyan malaman muslunci.

“Dagan an sai na shiga kogin tunani, nayi nayi in hana kai na, amma ina, wani abu na fada min lallai sai na koma musulunci. Daga nan sai na bayyana ma abokina Qunber Ali abin dake damuna.” Inji Jermaine.

'Ɗan uwan Michael Jackson, Jermaine ya musulunta
Michael Jackson tare da Jermaine

“Bayan karbi musulunci sai na fahimci amsoshin tambayoyin da na kasa amsa ma kai na cikin addinin kirista, a cikin musulunci ne na gane asalin hakikanin haihuwar Annabi Isa, sai hankalina ya kwanta dangane da addinin. Ina fatan dangina zasu fahimci gaskiyar da na gani a muslunci, saboda su mabiya darikar Jehovah witness ne na addinin kirista.

“A cewar addinin nasu, mutane 144,000 ne kadai zasu samu shiga aljanna, ta yaya? Na tambayi kai na. nayi mamaki matuka ganin yadda ashe ma Bible din zamanin nan mutane da dama ne suka hada shi, toh ta yaya mutum zai hada littafi kuma yace Allah ne ya saukar da shi. A zaman da nayi a Saudi Arabia, na siya kasukan malamin nan mai suna Yusuf Islam, kuma na karu sosai.” Inji shi

'Ɗan uwan Michael Jackson, Jermaine ya musulunta
Michael Jackson tare da Jermaine suna waka

A wata hira da Jermaine yayi da BBC yace da ace Michael ya kai yanzu, toh da ya musulunta: “Ina tsammanin da Michael ya musulunta da ya kai yanzu, kuma ina da hujjoji na.

“Me yasa? Idan kana tabbacin kai wanene, kuma kasan su waye tare da kai, abubuwa zasu fara canza maka yadda ya dace. Abin kawai shine mutum ya zamto mai karfin imani, Allah gagara misali ne.” in ji Jermaine.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani bishiya da sunan Allah ya bayyana a jikinta

Asali: Legit.ng

Online view pixel