Yau aka cika shekaru 9 da rasuwar fitaccen Mawaki Micheal Jackson

Yau aka cika shekaru 9 da rasuwar fitaccen Mawaki Micheal Jackson

A rana irin ta yau watau 25 ga Watan Mayu ne aka cika shekaru 9 cif da rasuwar fitaccen Mawakin nan kuma Makadi kuma Mazarin da ba a taba yin irin sa ba inji wasu Masana watau Micheal Jackson.

Yau aka cika shekaru 9 da rasuwar fitaccen Mawaki Micheal Jackson

Micheal Jackson lokacin da yake wasa shekarun baya

Dalilin haka ne mu ka kawo maku wasu abin tunawa game da rayuwar Marigayi Michael Jackson wanda Duniya tayi rashin sa. Michael Jackson Attajiri ne kuma ko bayan mutuwar sa, wakokin sa sun cigaba da yin kasuwa a Duniya.

1. Mutuwar sa

Michael Jackson ya cika ne a Kasar sa ta Amurka yana da shekaru 50 a Duniya a 2008 bayan ya samu bugawar zuciya. Mutuwar Bajimin Mawakin ta rikita Duniya inda har sai da wasu kafafen sadarwa na yanar gizo su ka girgiza a ranar.

KU KARANTA: Yadda na tsallake barazanar lalata a Jami'ar Bayero

2. Aure

Michael Jackson yayi aure har sau 2 sai dai a ko yaushe auren bai wuce shekaru 2 ko 3. A 1994 ya auri Lisa Presley amma su ka rabu a 1996, daga nan kuma ya koma ya auri Debbie Rowe wanda su ka rabu bayan shekara 3. Ya rasu ya bar ‘Ya ‘ya 3 a Duniya.

3. Shahara

“Guinness World Records” ta tabbatar da cewa duk a tarihin Duniya ba a taba samun wanda yayi suna ya samu karbuwa kamar Michael Jackson ba. Babban Mawakin ya samu kyaututtuka da sun fi a kirga a harkar waka har bayan mutuwar sa.

4. Rawa

Michael Jackson ya kware a bangaren rawa kamar mazari wanda har ta kai yake wani irin rawan da shi kadai ya iya a Duniya. Wata sa’ar sai ka ga Michael kamar ya rabu da iska idan yana tika rawa a gaban Masoyan sa.

5. Bakar fata

Asalin Michael Jackson bakar fata ne amma ya rikida ya zama fari. Michael Jackson shi ne Bakin Mawakin farko da aka fara saka wakokin sa a Tashar MTV. Asali tare da 'Yan gidan su ya fara waka lokacin yana karamin yaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel