An Yi Rashi: Fitaccen Ɗan Wasan Kokowa na Duniya, Hogan Ya Mutu Yana da Shekaru 71

An Yi Rashi: Fitaccen Ɗan Wasan Kokowa na Duniya, Hogan Ya Mutu Yana da Shekaru 71

  • Hulk Hogan, tauraron wasan kokawa kuma masoyin Donald Trump, ya rasu yana da shekara 71 bayan bugun zuciya a gidansa
  • WWE ta tabbatar da mutuwarsa, inda ta tuna da gudummawar da Hogan ya bayar wajen yada wasan kokawa tun shekarun 1980
  • Bayan fuskantar cece-kuce da dama, Hogan ya koma siyasa, inda aka gansa a gangamin Trump 2024 sannan ya fito a fina-finai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Hulk Hogan, tauraron kokowar nan wanda ya shahara a duniya kuma ya kasance babban magoyin bayan Donald Trump, ya rasu yana da shekaru 71.

An ce Hogan, wanda sunansa na gaskiya shi ne Terry Gene Bollea, ya samu bugun zuciya ne a gidansa da ke Clearwater, Florida, inda ya rasu a gaban iyalansa.

Fitaccen ɗan wasan kokowa Hulk Hogan, masoyin Donald Trump, ya rasu yana da shekaru 71
Fitaccen ɗan wasan kokowa Hulk Hogan yayin da yake motsa jiki a ranar 28 ga Janairun 2025. Hoto: @HulkHogan
Source: Twitter

An ta yada jita-jitar rasin lafiyar Hulk Hogan

Kara karanta wannan

'Za su iya tarwatsa jihar Kano': NAFDAC ta ƙwace sinadaran haɗa abubuwan fashewa

Ko kafin mutuwarsa, jaridar The Guardian ta rahoto cewa an dade ana yada jita-jita game da lafiyarsa, inda aka ce an kwantar da shi a asibiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mako guda da ya gabata, matarsa Sky ta musanta jita-jitar cewa ya fada doguwar suma, tana mai cewa zuciyarsa na da ƙarfi duk da shan tiyata da dama da ya yi.

An fi gane Hogan da gemu mai rawaya da ke zagaye da bakinsa da daura kyalle a kansa. Yana ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan kokowa na shekarun 1980, kuma ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin mafiya girma a tarihin wannan wasa.

Tare da girmansa da tasirin sa a cikin filin wasa, Hogan ya taimaka wajen sauya wasan kokowa zuwa na nishaɗin gida, musamman ta hanyar haɗin guiwa da kamfanin WWE.

An sanar da rasuwar dan kokowa, Hogan

Kamfanin WWE ya tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, yana cewa:

“WWE na cikin jimami da samun labarin rasuwar Hulk Hogan, wanda yake da matukar girma a WWE. Hogan ya taimaka wajen kai WWE ga matakin duniya tun a shekarun 1980. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, abokansa da masoyansa.”

Kara karanta wannan

Ana maganar takarar Pantami, Gwamna Inuwa ya yi tsokaci kan magajinsa a Gombe

A 1996, Hogan ya kafa New World Order (NWO) kuma ya koma kiran kansa da Hollywood Hulk Hogan.

An shigar da shi cikin kundin sanannun 'yan wasan WWE na duniya a 2005, amma daga baya aka cire shi saboda wata rigima da ta biyo bayan fitar wani bidiyo da aka ɗauka a ɓoye yayin da yake tare da wata mata, inda aka jiyo kalaman wariya daga bakinsa.

Shafin Gawker ya fara wallafa bidiyon a shekarun 2010, daga bisani Hogan ya kai ƙara, ya yi nasara a kotu kuma hakan ya tilasta shafin daina aiki.

Hulk Hogan na daya daga cikin wadanda suka samu shiga kundin WWE na duniya
Hulk Hogan ya keta rigara kamar yadda ya saba a wasan WWE, inda ya bayyanar rigar Trump 2025. Hoto: @HulkHogan
Source: Getty Images

Kadan daga fadi tashin Hulk Hogan

An sake shigar da shi cikin kundin WWE na duniya a 2020, bayan da ya zama ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan gangamin siyasar MAGA na Donald Trump.

A taron gangamin jam’iyyar Republican na 2024, Hogan ya fito yana keta rigarsa kamar yadda ya saba a wasan WWE, inda ya bayyana rigar Trump 2024 a jikinsa.

Hogan ya ci gaba da kasancewa ɗan wasan kwaikwayo, inda ya fito a fim ɗin Rocky III na 1982 a matsayin Thunderlips, da kuma fina-finai kamar No Holds Barred, Suburban Commando da Mr Nanny.

Kara karanta wannan

"Ta ɗauki wuka, ni na ɗauki guduma": Saurayi ya faɗi yadda ya kashe budurwarsa

Daga 2005 zuwa 2007, ya fito a cikin shirin gaskiya na VH1 mai suna Hogan Knows Best, tare da tsohuwar matarsa Linda da ’ya’yansa Brooke da Nick.

WWE: Soyayyar Trump ga wasan kokowa

A wani labarin, mun taba rahoto cewa Shugaba Donald Trump ya kasance masoyin wasan kokowa na WWE ko kuma gasar Wrestlemania mai farin jini.

A wasu shekaru da suka gabatam kafin ya soma karade jihohin Amurka yakin neman zabe, Donald Trump ya taba shiga gasar hamshakan attajirai na wasan kokowa ta WWE.

Bayanai sun nuna cewa, Trump ya taba shiga wata caca da shugaban ‘yan kokawar Vince Mc Mahon kuma shugaban kasar ya lashe gasar, amma an ce da magudi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com