Trump da wasan Kokawan WWE a Amurka
Daya daga cikin da abin da Donald Trump wanda ya lashe zaben shugabancin Amurka ya shahara a kai shi ne iya ta da kura a musamman a gaban kyamara, hakan ta bayyana ne a wani wasan kokawa na WWE da ake yi a kasar a inda ya taka rawa a shekarun baya
Kimanin Shekaru tara da suka gabata kafin ya soma karade jihohin Amurka yakin neman zabe, Donald Trump ya taba shiga gasar hamshaken attajirai na wasan kokowa ta WWE ko Wrestlemania mai farin jini.
Bayanai sun nuna cewa, Trump ya taba shiga wata caca da shugaban ‘yan kokawar Vince Mc Mahon a inda ya kuma lashe da magudi.
Mc Mahon da Trump sun nemi ‘yan wasan kokawa Bobby Lashley da Umaga su kara a tsakaninsu, a wasan gasar kokawar na shekara na Wrestlemania, amma Trump kuma shugaban mai jiran gado a yanzu, ashe ya shirya tsiya ta hanyar shigo da wani dan kokawa Stone cold Steve Austin ta bayan gida.
KU KARANTA KUMA: Donald Trump ya kerewa Hillary Clinton a zaben Amurka
Dan kokawa Austin Stone cold ya shigo filn kokawar ne a matsayin alkalin wasa, ya kuma hana Umaga cin wasan kafin da ga baya Lashley ya samu ya yiwa abokin karawarsa kaye.
Trump da kuma Mc Mahon sun yi ‘yar wata karawa a bayan fage, ya kuma yi masa askin dole duk a cikin lashe caca da suka yi.
Asali: Legit.ng