Abubuwa na cigaba da faruwa a Saudiyya: An gabatar da wasan kokawa na 'yan Amurka wato WWE a birnin Jiddah
- Wannan dai shine karo na farko da kungiyar kokawa ta Amurka WWE ta shirya wani gagarumin wasa a birnin Jiddah dake kasar Saudi Arabia.
Wannan dai shine karo na farko da kungiyar kokawa ta Amurka WWE ta shirya wani gagarumin wasa a birnin Jiddah dake kasar Saudi Arabia. Shahararren dan wasan kokawar nan na kasar Amurka John Cena shine ya zama gwarzon wasan a wata karawa da yayi da abokin wasan sa Triple H a babban filin motsa jiki na Sarki Abdullah dake birnin Jiddah.
DUBA WANNAN:A bisa dukkan alamu dai Dino Melaye zai samu nasara a kiranyen da ake yi masa
An yada wannan gasar wacce ta samu karbuwa sosai daga al'ummar Saudiyya, inda kai tsaye aka dinga yadawa a tashoshin talabijin na gwamnatin kasar da kuma tashoshi na masu zaman kansu.
Ministan wasanni na kasar ta Saudiyya, Turki bin Abdulmuhsin Al Sheikh ya rattaba hannu a wata yarjejeniya da suka yi da kungiyar kokawan ta WWE, yarjejeniyar wacce zata kai tsawon shekaru 10, da nufin shirya irin wadannan wasannin a kasar.
Kusan 'yan kokawa 50 ne wadanda suka samu damar halartar wurin wasan zasu kara da juna domin fidda gwani.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng