Saudiyya: A ƙarshe, Ɗan Sarki Ya Rasu bayan Dogon Suma na Tsawon Shekaru 20
- Yarima Al-Waleed bin Khaled ya rasu bayan shekaru 20 cikin dogon suma da ya faru bayan hatsarin mota a London
- Mahaifinsa, Prince Khaled, ya tabbatar da rasuwar ɗansa, yana cewa sun yarda da ƙaddara bayan rashin ɗansu
- Za a yi sallar jana’izarsa a Riyadh ranar Lahadi, bayan sallar la’asar, sannan za a shiga zaman makoki na kwanaki uku
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Riyadh, Saudiyya - A karshe, dan Sarki a kasar Saudiyya, Yarima Al-Waleed bin Khaled bin Talal Al Saud ya rasu.
Marigayin, wanda aka fi sani da ‘Sarkin Barci’ ya rasu bayan shekaru 20 cikin dogon suma da ya yi.

Source: Twitter
Bayan shekaru 20 a sume, dan Sarki ya rasu
Yariman ya rasu ne a Asibitin King Abdulaziz 'Medical City' da ke Riyadh, kamar yadda Inside the Haramain ta wallafa a X.

Kara karanta wannan
'Zai yi wahala Obi ya yi shugaban kasa,' Hadimin Buhari ya yi martani ga Obidients
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ajiye marigayin tun shekaru 20 da suka wuce watau 2005 bayan mummunan haɗarin mota da ya gamu da ita.
Yariman ya samu haɗarin ne a London yana karatu a makarantar soja, inda rauni ya jawo masa zubar jini a kwakwalwa.
Mahaifinsa, Prince Khaled bin Talal bin Abdulaziz Al Saud, ya tabbatar da labarin rasuwar cikin alhini da yarda da ƙaddarar Allah.
Ya rubuta cewa:
“Da zukatan da suka aminta da ƙaddarar Allah, muna alhini kan rasuwar ɗanmu, Allah ya jikansa.”
Fadar Sarautar Saudiyya ta tabbatar da rasuwar, inda ta ce za a yi sallar jana’iza ranar Lahadi bayan sallar la’asar a Riyadh.
Za a yi jana’izar ne a Masallacin Imam Turki bin Abdullah, sannan za a ci gaba da zaman makoki na kwanaki uku.
Lamarin yariman ya jawo hankalin duniya saboda lokutan da yake motsa hannaye ko kai, wanda ke ƙara fata ga iyalinsa.
Yarima Khaled ya kasance tare da ɗansa a kai a kai, yana yada bidiyoyi da sababbin bayanai tare da neman addu’ar jama’a.
Soyayya da ƙwarin guiwar mahaifinsa sun sa labarinsa ya zama na juriya da sadaukarwa a kasashen Larabawa.

Source: AFP
Alakar marigayin da Sarki Salman na Saudiyya
A ‘yan shekarun nan an rika rade-radin cewa ya farfaɗo, amma babu wani tabbaci yayin mutuwarsa ta kawo ƙarshen jita-jitan.
Al-Waleed bin Khaled bin Talal yana cikin dangin sarakunan Saudiyya, amma ba ɗa ko ɗan'uwan Sarki Salman ba ne kai tsaye.
Kakansa, Talal bin Abdulaziz Al Saud, ɗaya ne daga cikin 'ya'yan Sarkin Abdulaziz Al Saud, wanda ya kafa kasar Saudiyya.
Saudiyya: Dan Sarki ya motsa bayan dogon suma
A baya, kun ji cewa dan Sarki, Al-Waleed bin Khaled bin Talal, wanda ake kira "Sarkin Barci," ya cika shekara 20 a duniya bai cikin hayyacinsa bayan hadarin mota a 2005.
An ce likitoci sun ba da shawarar a cire na'urorin taimakon numfashi a 2015, amma mahaifinsa ya ki, yana fatan samun sauki.
A 2019, Al-Waleed ya dan yi motsi kamar daga yatsa ko juya kai, amma rahotanni sun ce ba a samu ci gaba ba bayan haka.
Asali: Legit.ng
