Tashin Hankali: Jirgin Sama Ya Yi Hatsari, an Nemi Direba da Fasinjoji an Rasa

Tashin Hankali: Jirgin Sama Ya Yi Hatsari, an Nemi Direba da Fasinjoji an Rasa

  • An shiga cikin tsananin tashin hankali da mamaki yayin da wani jirgin sama kirar Cessna 182 ya yi hatsari a yankin Elberta, da ke kasar Alabama
  • Hukumar kashe gobara ta Elberta ta kai daukin gaggawa wurin da jirgin ya fadi, amma ba a tarar da matuki ko kuma fasinjo ko daya ba, sai dai jini
  • Hukumomi sun fara bincike don gano dalilin hatsarin da kuma inda mutanen da ke cikin jirgin suka shiga yayin da aka nemi taimakon jama'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Alabama - An gano wani jirgin sama samfurin Cessna 182 da ya yi hatsari a wani filin jirgin sama da ke Alabama ba tare da an ga matuƙin jirgin ko fasinjojin cikinsa ba.

Da sanyin safiyar Juma'a, hukumar kashe gobara ta Elberta ta amsa kiran da aka yi mata game da wani hatsarin jirgin sama a Baldwin County - wanda ke gabar tekun Gulf, gabas da Mobile.

Kara karanta wannan

Tsaurin ido: An cafke matasa 4 kan zargin gagarumar sata a majalisar tarayya

An samu wani hatsarin jirgin sama a Alabama, amma an nemi matuki da fasinjoji an rasa
An rasa matuƙin jirgin da fasinjoji bayan wani mummunan hatsarin jirgin sama da ya faru. Hoto: NurPhoto/GettyImages
Source: Getty Images

Wadanda suka kira hukumar, sun bayyana cewa wani ƙaramin jirgin sama ya faɗi a yankin, kamar yadda rahoton WPMI News ya bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma da mahukunta suka isa wurin, sun tarar da jirgin saman a kife, an kuma ga jini ya fallasa ta ko ta ina, ga karikitan jirgin da suka warwatse ba tare da alamar matuƙin ba, ko wani fasinja.

Abubuwan da aka gano a wajen hatsarin

Daraktan hukumar kula da iftila'i na Baldwin County, Tom Tyler, ya ruwaito cewa fiffiken jirgin ya lalace, wataƙila saboda ya ci karo da ƙasa, kuma yana ɗauke da kimanin galan 50 na mai, kuma bai zube ba.

Hukumomi ba su sami wata alama ta nan take game da matuƙin jirgin ko kuma fasinjoji ba, inda Tyler ya lura cewa:

"Jirgin ya kife ne, amma ba mu tarar da kowa a ciki ba. Muna zargin ko sun bar wurin da kafafunsu, ko an zo an kawo masu dauki."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace amarya awa 2 kafin ɗaurin aurenta, sun bindige yayanta

Rahoton AL.com ya nuna cewa jirgin yana shawagi a kusa da Orange Beach kafin ya nufi Arewacin yanki ya ɓace daga tsarin bin diddigin jirage.

Ana sa ran hukumar kula da jiragen sama ta tarayya (FAA) za ta ci gaba da bincike, inda jami'ai za su isa mako mai zuwa don bincikar tarkacen jirgin.

An nemi fasinjoji da direba an rasa bayan jirgin sama ya yi hatsari a Alabama
Wani jirgin sama da ya yi hatsari, ya dare gida biyu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yawaitar hatsarin jirgin sama a Baldwin

Rashin matuƙin jirgin da kuma alamun jini sun haifar da hasashe, amma ba a bayar da rahoton raunuka ko mace-mace ba har zuwa ranar 29 ga Yuni, 2025.

Ofishin Sheriff na Baldwin County da FAA suna ci gaba da binciken don gano musabbabin hatsarin jirgin da kuma inda mutanen da ke ciki suka shiga.

Wannan lamarin ya ƙara shiga tarihin yawaitar faɗuwar jirage a Baldwin County, kamar faɗuwar wani jirgin ruwa na Navy T-6B Texan II a 2020 da kuma wani hatsarin jirgin horo a 2023, sun haɗa da yanayi daban-daban da nau'ikan jirage.

Mutane 8 sun mutu a hatsarin jirgin sama

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fasinjoji shida da ma'aikatan jirgi biyu sun mutu a hatsarin jirgin da ya faru a Ribas, a cewar rundunar 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Mota dauke da bam ta tarwatse a Kano, mutum 5 sun kwanta dama

Hakan na zuwa ne bayan hukumar tsaro ta tabbatar da mutuwar uku daga cikin fasinjojin, inda aka tsamo gawarwakinsu a kogi.

Bayan faruwar hatsarin, shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni na a tsananta bincike domin gano sauran fasinjojin jirgin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com