Rahoton Sirri Ya Karyata Ikirarin Trump na Ruguza Cibiyar Nukiliyar Iran

Rahoton Sirri Ya Karyata Ikirarin Trump na Ruguza Cibiyar Nukiliyar Iran

  • Sabon rahoton leƙen asirin Amurka ya nuna cewa harin da sojojin Amurka suka kai kan wuraren nukiliyar Iran bai lalata cibiyoyin ba gaba ɗaya
  • Wani rahoto daga hukumar leƙen asirin tsaro ta soji ta Amurka (DIA) ya nuna cewa harin ya jinkirta shirye-shiryen Iran na nukiliya ne kawai na ƴan watanni
  • Sai dai shugaban kasar Amurka, Donald Trump musanta rahoton, yana cewa harin ya yi nasara kuma an cimma burin lalata shirin nukiliyar Iran

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Rahoton leken asirin Amurka ya nuna cewa hare-haren da ta kai a kan cibiyoyin nukiliyar Iran ba su kai ga lalata gaba ɗaya shirin Iran na nukiliya ba.

Rahoton ya ce harin zai jinkirta shirin ne kawai na ƴan watanni, ba tare da samun nasarar rusa komai baki ɗaya ba.

Kara karanta wannan

Iran ta fadi mataki na gaba bayan lalata sassan wurin kera makamin nulkiliyarta

Bincike ya karyata ikirarin Amurka na rusa cibiyar nukiliyar Iran
Bincike ya karyata ikirarin Amurka na rusa cibiyar nukiliyar Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton da CNN ta wallafa da ya samo tushe daga bayanan sirri da Hukumar Tsaron Amurka ta DIA ta tattara ya tabbatar da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

DIA ta bayyana haka ne a cikin rahoton yayin tantance irin barnar da aka yi wa cibiyoyin da kuma tasirin hakan ga burin Iran.

Donald Trump ya musa rahoton DIA kan Iran

Ko da yake shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a bainar jama’a cewa an “rushe gaba ɗaya” shirin nukiliyar Iran, rahoton DIA ya saba da hakan.

Wasu daga cikin rahotonni sun bayyana cewa Iran ta rigaya ta fitar da sinadarai masu ƙarfi daga wuraren kafin harin.

Wani masani ya ce:

“Rahoton na nuna cewa harin da aka kai bai fi jinkirta shirin Iran da watanni kaɗan ba.”

Sai dai fadar White House ta musanta rahoton, inda mai magana da yawun fadar, Karoline Leavitt, ta ce:

"Rahoton ba daidai ba ne kuma wani matsakaicin jami’i ne ya fitar da shi don bata sunan shugaba Trump.”

Kara karanta wannan

Trump ya magantu kan sauya gwamnatin Iran, ya faɗi abin da zai tilasta faruwar haka

Barnar da Amurka ta yi a cibiyar nukiliyar Iran

Rahotanni sun ce an yi babbar barna a manyan gine-ginen sama na wuraren nukiliyar da aka kai wa hari – ciki har da Fordow, Natanz da Isfahan.

Rahoton BBC ya nuna cewa barnar ta shafi injinan wutar lantarki da wasu gine-gine da ake sarrafa sinadaran nukiliya da su.

Amma babban abin da ke jawo ce-ce-ku-ce shi ne cewa, na’urori da sinadaran nukiliya masu ƙarfi ba su lalace ba kamar yadda aka yi ikirari a farko.

Kasar Amurka ta ce harin ya samu nasara sosai, inda aka yi amfani da bama-baman a kan wuraren.

Trump ya doge kan rusa cibiyar nukiliyar Iran
Trump ya doge kan rusa cibiyar nukiliyar Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaba Trump, da ke halartar taron NATO a Netherlands, ya bayyana cewa:

“An rushe cibiyoyin nukiliyar Iran gaba ɗaya!”

Har yanzu hukumar leƙen asirin Amurka na ci gaba da tattara bayanai daga cikin Iran domin tantance hakikanin barnar da aka yi.

Iran za ta cigaba da hada nukiliya

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta yi magana kan makomar wuraren nukiliyarta bayan tsagaita wuta da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Amurka ta ɗebo ruwan dafa kanta, wasu ƙasasshe sun shirya ba Iran makaman nukiliya

Gwamnatin Iran ta ce ba gudu ba ja da baya kan cigaba da kera makaman nukiliya domin kare kanta.

Hakan na zuwa ne bayan shafe sama da kwanaki 10 Iran na gwabza fada tsakaninta da Isra'ila kan mallakar manyan makamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng