Ana cikin Murnar Tsagaita Wuta, Bam Ya Tarwatse da Sojojin Isra'ila a Zirin Gaza
- Isra'ila ta sanar da mutuwar sojojinta bakwai a Kudancin Zirin Gaza bayan wani bam mai karfi ya tarwatse a motar da suke tafiya a cikinta
- Harin da Hamas ta ɗauki alhakinsa ya zama ɗaya daga cikin mafi muni ga sojojin Isra'ila a rikicin Gaza tun bayan barkewar fadan a 2023
- Hukumar sojin Isra'ila ta ruwaito cewa, akalla sojojinta 860 suka mutu tun bayan barkewar yaƙinta da Gaza, yayin da dubunnai suka jikkata
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Isra'ila - Isra'ila ta bayyana cewa an kashe sojojinta bakwai, wani babban jami'i da wasu kananun sojoji shida, a yayin faɗa a Kudancin Zirin Gaza a ranar Talata.
Sojojin Isra'ilan bakwai, waɗanda duk 'yan bataliyar Combat Engineering ta 605 ne, sun mutu lokacin da wani bam mai ƙarfi ya tashi a kan motar yaƙi kirar Puma, inda ta kama da wuta.

Source: Getty Images
Kokarin kashe wutar ya ci tura, inda dukansu bakwai din suka mutu, yayin da aka dauko motar da ta ƙone daga Gaza daga baya, kamar yadda rahoton Reuters ya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin Hamas da daukar fansar Isra'ila
A wani harin na dabam a yankin, wasu sojoji sun samu raunuka sakamakon harbin roka (RPG), inji sanarwar da hukumar sojin IDF ta fitar ranar Laraba.
Harin, wanda ƙungiyar Al-Qassam ta Hamas ta ɗauki alhakinsa, ya zama ɗaya daga cikin mafi muni ga sojojin Isra'ila a rikicin Gaza da ke gudana, wanda ya fara ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Yaƙin Gaza ya fara ne lokacin da 'yan ta'addar Hamas suka kai hari Isra'ila, inda suka kashe mutane 1,200 tare da rike mutane 251, a cewar rahoton Isra'ila.
Hare-haren sama da na kasa na Isra'ila sun yi kaca-kaca da Gaza, inda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ba da rahoton mutuwar Falasɗinawa sama da 56,000, sannan mutane kusan miliyan 2 sun rasa matsugunansu.
An kashe sojojin Isra'ila 860 a rikicin Gaza
Hamas ta bayyana cewa mayakanta sun yi wa sojojin Isra'ila kwanton bauna a Khan Younis, inda suka kai hari kan sojin a wani gini da makami mai linzami kirar Yassin 105.

Source: Getty Images
IDF ta ba da rahoton mutuwar sojoji 19 a Gaza a watan Yunin 2025, inda ta ce an kashe jimillar sojojinta 860 tun farkon yaƙin, ciki har da sama da 400 da aka kashe a Gaza.
Sojojin IDF na ci gaba da rushe kayan yakin Hamas, yayin da suke zargin ƙungiyar da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa da kuma rusa yarjejeniyar rarraba kayan agaji.
Trump ya fusata da harin Isrra'ila kan Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump, ya bayyana rashin jin daɗinsa ga Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, bayan Isra’ila ta sake kai hari kan Iran.
Donald Trump ya riga ya gargaɗi Isra’ila da kada ta ƙara kai hari, amma duk da haka, ta ƙi sauraro, abin da ake zargin ya jawo rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta.
Rahotanni sun bayyana cewa Trump na jin kamar Netanyahu ya yaudare shi, duk da ƙoƙarin da ya yi na sasanta Isra’ila da Iran da kuma dawo da zaman lafiya a kasashen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

