Ana Batun Tsagaita Wuta, Sarkin Qatar Ya Yi Magana da Shugaban Iran Ta Wayar Tarho

Ana Batun Tsagaita Wuta, Sarkin Qatar Ya Yi Magana da Shugaban Iran Ta Wayar Tarho

  • Sarkin Qatar, Sheikh Tamim Bin Hamad Al Thani ya yi magana da shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ta wayar tarho
  • Firaministan ƙasar Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani ya ce shugabannin biyu sun tattauna kan batun harin Al Udeid
  • Sarkin Qatar ya nuna damuwa kan yadda Iran mai makwaftaka da su ta zaɓi kai wa ƙasarsa hari, yana mai cewa ya kamata a kawo ƙarshen lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Qatar - Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya kira sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ta wayar tarho bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Sarkin da shugaban Iran sun tattauna kan harin da Jamhuriyar Musuluncin ta kai sansanin sojojin Amurka na Al Udeid da ke cikin Qatar.

Sarkin Qatar da shugaban ƙasar Iran.
Sarkin Qatar ya tattauna da shugaban Iran ta wayar tarho Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani ne ya bayyana hakan ranar Talata, 24 ga watan Yuni, kamar yadda Al-Jazeera ta tattaro.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya bijirewa umarnin Trump, ya ba sojoji umarnin kai wa Iran hare hare

Me Sarkin Qatar ya tattauna da shugaban Iran?

Sheikh Mohammed ya tabbatar cewa Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya karɓi kiran waya daga Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.

Ya ƙara da cewa jagororin biyu sun maida hankali wajen tattaunawa kan batun harin da Iran ta kai sansanin sojin ƙasar Amurka na Al Udeid, cewar BBC News.

Sheikh Muhammed ya ce sarkin ya jaddada cewa Qatar na bin ka’idar zaman makwabtaka kuma bai taɓa tsammanin irin wannan farmaki na ƙiyayya daga Iran ba.

Har ila yau, Sheikh Mohammed ya bayyana cewa sarkin ya yi magana kan cewa Qatar na da damar daukar matakin diflomasiyya da na shari’a kan Iran bisa wannan hari.

Amma ya jaddada wa shugaban ƙasar Ira, yayin tattaunawarsu a waya, cewa, “ya kamata a warware matsalar cikin gaggawa kuma a manta da ita gaba ɗaya.”

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.
Qatar ta bukaci kasashen duniya su haɗa kai don kawo karshen rigingimun Gabas ta Tsakiya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abin da ke jawo rikici a Gabas ta Tsakiya

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya maida martani bayan Iran ta kai hari kan sansanin sojin Amurka

Ya kuma danganta rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya da sakamakon faɗaɗar hare-haren cin zarafin da Isra'ila ke kai wa a Gaza, wanda Qatar ke ƙoƙarin hana ya bazu zuwa sauran sassa.

Firaministan Qatar, Sheikh Mohammed ya ƙara da cewa:

“Lokaci ya yi da duniya baki ɗaya za ta haɗa kai wuri guda domin kawo ƙarshen waɗannan munanan ayyuka na rashin da’a da Isra’ila ke aikatawa a yankin."

Ya kuma sake nanata matsayar Qatar na Allah wadai da harin da Iran ta kai sansanin sojin Amurka da ke ƙasar, yana mai cewa bai kamata hakan ta faru ba.

Su wa ke neman ruguza tsagaita wuta?

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya ce duka ƙasashen Isra'ila da Iran sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma

Sai dai Shugaba Trump ya ƙara ɗora wa Isra'ila laifi, inda ya bukaci ta umarci duka matuƙan jiragen yakinta su dawo gida.

Donald Trump ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yadda kasashen biyu ke ci gaba da harbawa juna makamai masu linzami duk da matsayar da aka cimma ranar Litinin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262