Farashin Man Fetur Ya Sauko Ƙasa bayan Isra’ila Ta Amince da Yarjejeniyar Trump

Farashin Man Fetur Ya Sauko Ƙasa bayan Isra’ila Ta Amince da Yarjejeniyar Trump

  • Farashin mai ya faɗi da sama da 5% bayan Isra'ila ta amince da tsagaita wuta da Iran, wanda ya rage fargabar kasuwar makamashi ta duniya
  • Farashin Brent da WTI sun sauko ƙasa sosai, yayin da kasuwannin Asiya da Turai suka farfaɗo, bayan sanarwar tsagaita wutar
  • Isra'ila ta cimma burinta na kawar da barazanar nukiliyar Iran, wanda ya rage tashin hankali kuma ya haifar da raguwar farashin mai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Isra'ila - Farashin danyen mai ya faɗi da sama da 5% a ranar Talata, bayan da Isra'ila ta sanar da amincewarta ga shawarar Shugaban Amurka, Donald Trump na tsagaita wuta da Iran.

Wannan matakin ya rage fargabar girgizar kasuwar makamashi da ta mamaye duniya sakamakon yaƙin kwanaki 12 tsakanin Isra'ila da abokiyar gabarta Iran.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Iran ta kai hari Isra'ila, 'ta rusa yarjejeniyar tsagaita wuta'

An samu faduwar farashin mai, musamman Brent da WTI bayan Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran
An samu faduwar farashin mai a duniya bayan Iran da Isra'ila sun tsagaita wuta. Hoto: Anton Petrus
Source: Getty Images

Farashin mai ya sauko ƙasa

A Asiya, farashin hannun jari ya tashi, yayin da kasuwannin Turai, musamman na London, Paris, da Frankfurt, suma suka tashi a safiyar Talata, inji rahoton Euro News.

Farashin man Brent ya faɗi da $2.48, ko kuma 3.5%, zuwa $69 a kan kowace ganga da misalin ƙarfe 09:27 agogon GMT. Man U.S. West Texas shi ma ya faɗi da $2.37, wato 3.5%, zuwa $66.14.

An samu saukar farashin dukkanin nau'ikan man guda biyu da kusan 5% a safiyar Talata bayan Trump ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran.

Dalilin faɗuwar farashin mai a duniya

Isra'ila ta amince da shawarar Trump na tsagaita wuta da Iran bayan ta cimma burinta na kawar da barazanar nukiliyar Tehran da kuma makamai masu linzami.

Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a ranar Talata, kamar yadda muka ruwaito.

Kara karanta wannan

Iran ta kashe mutane a harin karshe zuwa Isra'ila, ta yaba da jarumtar sojojinta

"Farashin mai ya faɗi sosai, saboda hare-hare da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran ba su haifar da faɗaɗa rikicin da zai iya zama barazana ga samar da kayan masarufi a yankin ba," inji Barclays a cikin wata sanarwa.

Yaƙin na kwanaki 12 ya haifar da tashin gwauron zabo a farashin mai, inda man Brent ya karu da kusan $10 a ranar Litinin, wanda shine mafi tsadarsa tun watan Yulin 2022.

Kasuwar duniya ta fara farfadowa bayan Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran
Wasu 'yan kasar Hong Kong na kallon yadda kasuwar hannun jari ke sauyawa. Hoto: Getty Images
Source: AFP

Kasuwannin duniya sun farfaɗo

DAX ya tashi da 1.99% zuwa 23,730.98, CAC 40 ya tashi da 1.71% zuwa 7,666.69, yayin da FTSE 100 ya tashi da 0.81% zuwa 8,828.83 a budewar kasuwar safiyar Talata.

Rahoton UK Finance ya nuna cewa STOXX 600 ya ƙaru da 1.48% zuwa 542.93, yayin da EURO STOXX 50 ya tashi da 1.9% zuwa 5,320.97.

A Amurka kuwa, hajojin S&P 500 sun tashi da 0.97% zuwa 6,135.75 a ranar Litinin, yayin da hajojojin Dow Jones suka ƙaru da 0.89% zuwa 43,284.00.

S&P/ASX 200 na Ostiraliya ya tashi da 0.89% zuwa 8,550.10, Kospi na Koriya ta Kudu ya tashi da 2.75% zuwa 3,097.28, kuma Shanghai Composite index ya haura da 1.07% zuwa 3,417.89.

Kara karanta wannan

Isra'ila da Iran sun amince su tsagaita wuta, Shugaban Amurka ya fitar da sanarwa

Hang Seng na Hong Kong ya tashi da 2% zuwa 24,162.70 kuma Nikkei 225 ya ƙaru da 1.16% zuwa 38,796.39.

US Dollar Index ya faɗi da 0.32% zuwa 98.10. Yuro ya sami karin 0.25% a kan dala yayin da Yen ya faɗi da 0.48% idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Iran ta kai hari Isra'ila bayan tsagaita wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakanin Isra’ila da Iran ta wargaje, bayan Isra’ila ta bayyana cewa Iran ta harba mata makamai masu linzami.

Ministan tsaron Isra’ila ya bayar da umarni ga dakarun kasar da su ci gaba da kai farmaki kan Tehran, yana mai cewa matakin ya zama dole bayan Iran ta karya yarjejeniyar.

Firayim Minista, Benjamin Netanyahu ya ce duk da Isra’ila ta amince da tsagaita wuta, za ta kare kanta da mayar da martani idan aka kai mata wani hari daga Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com