Tashin Hankali: Iran Ta Kai Hari Isra'ila, 'Ta Rusa Yarjejeniyar Tsagaita Wuta'

Tashin Hankali: Iran Ta Kai Hari Isra'ila, 'Ta Rusa Yarjejeniyar Tsagaita Wuta'

  • Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma wa tsakanin Isra'ila da Iran ta rushe bayan Isra'ila ta ce Iran ta harba mata makamai masu linzami
  • Ministan tsaron Isra'ila ya umarci sojoji su ci gaba da kai hare-hare kan Tehran bayan rusa yarjejeniyar tsagaita wutar da Iran ta yi
  • Firayim Minista, Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila ta amince da tsagaita wutar, amma za ta mayar da martani idan Iran ta kai mata wani hari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Isra'ila - Yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi da Shugaba Donald Trump ya gabatar ta samu tangarɗa yayin da Isra'ila ta ce Iran ta harba mata makamai masu linzami.

Isra'ila ta yi ikirarin cewa Iran ta harba makaman zuwa sararin samaniyarta kasa da sa'o'i uku bayan fara aikin tsagaita wutar, kuma ta sha alwashin ɗaukar fansa.

Kara karanta wannan

Yaki zai dawo sabo: Isra'ila ta ce za ta cigaba da kai hari Iran bayan tsagaita wuta

Isra'ila ta tabbatar da cewa Iran ta harba mata makamai masu linzami awanni bayan kulla yarjejeniyar tsagaita wuta
Wasu makamai masu linzami da Iran ta harba sun sauka a Tel Aviv, babban birnin Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ana zargin Iran ta kai hari a Isra'ila

An ji fashe-fashe da tashin ƙararrawar gargadi a faɗin Arewaci da Tsakiyar Isra'ila da safiyar Talata, kamar yadda rahoton AP News ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dai na zuwa ne bayan da Isra'ila da Iran sun amince da yarjejeniyar tsagaita wutar don kawo ƙarshen abin da Trump ya kira da "yaƙin kwanaki 12".

Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya kira harba makamai masu linzami da Iran ta yi a matsayin rusa yarjejeniyar tsagaita wutar.

Israel Katz ya kuma umarci sojojin Isra'ila da su ci gaba da "shiri mai tsanani don kai hari Tehran da lalata gine-ginen gwamnati da cibiyoyin makamai."

Kai hare-hare bayan yarjejeniyar tsagaita wuta

Tsakanin saƙon Trump da fara tsagaita wutar, Isra'ila ta kai jerin hare-hare ta sama da suka shafi wurare a faɗin Iran kafin alfijir, kuma Iran ta mayar da martani da ruwan makamai masu linzami waɗanda suka kashe akalla mutane huɗu a Isra'ila da sanyin safiyar Talata.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta amince da tsagaita wuta, ta gargadi Iran kan kai mata hari

Isra'ila ta ce ta tare harin makamai masu linzami na Tsakiyar kasar a safiyar Talata wanda ya zo sa'o'i kaɗan bayan fara tsagaita wutar.

"Tehran za ta girgiza" ministan kuɗin Isra'ila, Betzalel Smotrich, ya rubuta a shafinnsa na X bayan an harba makamai masu linzamin.

Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran, amma ba za ta lamunci wani harin ba
Firayin Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu | Shugaban koli na kasar Iran, Ali Hosseini Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Netanyahu ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta

Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila ta amince da tsagaita wutar tsakanin ta da Iran Iran, bayan sa bakin Shugaban Amurka, Donald Trump.

Ya ce ya faɗa wa majalisar tsaron Isra'ila cewa ƙasar ta cimma dukkan burikan yaƙinta, ciki har da kawar da barazanar shirin nukiliyar Iran da na makamai masu linzami.

Isra'ila ta kuma kashe shugabancin sojojin Iran da dama tare da lalata shugabancin gwamnati, kuma ta samu iko kan sararin samaniyar Tehran, in ji Netanyahu.

Iran ta yabawa sojojinta kan farmakar Isra'ila

A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa ƙasarsu ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Donald Trump ya kawo.

A cewarsa, Iran ta ci gaba da kai hare-haren dakarunta har zuwa ƙarfe 4:00 na safe, mintuna kaɗan kafin fara tsagaita wutar da aka cimma a ranar Litinin.

Araghchi ya yaba da ƙoƙarin dakarun Iran, yana mai jinjina musu bisa tsayin daka da jajircewa wajen kare martabar ƙasa har zuwa lokacin da aka amince da dakatar da farmaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com