Tsohon Shugaban Amurka Ya Tona Asirin Benjamin Netanyahu kan dalilin Yaƙar Iran
- Tsohon Shugaban Amurka, Bill Clinton, ya yi tone-tone kan rigimar da ke faruwa tsakanin kasashen Iran da Isra'ila a yanzu
- Clinton ya ce Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana amfani da yakin Iran domin ya ci gaba da mulki har abada
- Tsohon shugaban ya bukaci Donald Trump da ya dakile rikicin Isra’ila da Iran, ya ce kashe fararen hula ba mafita ba ce
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, Amurka - Tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton, ya yi magana kan harba makamai da ake cigaba da yi tsakanin Iran da Isra'ila.
Bill Clinton da ya bar ofis a 2011 ya ce Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da gangan yake yakar Iran saboda cimma burinsa.

Source: Getty Images
Clinton ya magantu kan fadan Iran, Isra'ila
Rahoton Arab News ya ce Clinton ya zargi Netanyahu yana son yin yaki da Iran domin ya ci gaba da mulki har abada.

Kara karanta wannan
'Yar Isra'ila ta rasa ranta sanadin bugun zuciya a harin makami mai linzami daga Iran
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Clinton wanda tsohon lauya ne shi ne shugaban Amurka na 42 wanda ya yi mulki daga shekarar 1999 zuwa 2001.
Game da yaƙin Iran da Isra'ila, Clinton ya ce:
“Netanyahu ya daɗe yana son yin yaki da Iran saboda hakan zai ba shi damar ci gaba da mulki har abada, ai, ya shafe kusan shekaru 20 a ofis."
Bill Clinton ya bukaci Shugaba Donald Trump da ya “kwantar da hankula” a rikicin Isra’ila da Iran.
Ya kuma roke shi ya kawo karshen kisan fararen hula kullum-kullum a tsakanin kasashen guda biyu da ake yi.
“Amma ina ganin ya kamata mu yi kokarin dakile wannan rikici, kuma ina fatan Shugaba Trump zai yi hakan."
- Cewar Clinton

Source: Getty Images
Clinton ya shawarci Trump kan fadan Iran, Isra'ila
Tsohon shugaban ya ce bai yi imani da cewa Netanyahu ko Trump na so a barke yaki gaba ɗaya a yankin ba.
Ya ce yana da muhimmanci Amurka ta kare abokanta a yankin, amma hakan bai kamata ta rika shiga yakin da ke hallaka fararen hula ba.
Ya kara da cewa:
“Muna bukatar mu tabbatar wa da abokanmu a Gabas ta Tsakiya cewa muna tare da su kuma za mu kare su.
“Amma zaɓar yaƙe-yaƙe ba tare da bayyanawa ba, inda fararen hula marasa hannu a ciki ke rasa rayukansu, ba mafita ba ce.”
Amurka har yanzu ba ta shiga kai tsaye cikin rikicin Iran da Isra’ila ba, amma ta taimaka wa Isra’ila harbo makamai daga Tehran.
Har ila yau, ta ba ta kayan aikin soja domin kare kanta a yayin da rikicin ke ci gaba, cewar rahoton Times of India.
Gwamnati ta musanta labarin kisan Shugaban Iran
Kun ji cewa kafofin sadarwa sun yi ta yada jita-jita ta yadu cewa an kashe tsohon shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad a birnin Tehran.
Wasu majiyoyi sun ce harin "na kwararru" ne, yayin da kafofin sada zumunta suka riƙa yada labarin mutuwarsa tare da iyalinsa.
Sai dai daga baya gwamnati ta karyata jita-jitar, ta tabbatar da cewa Ahmadinejad yana raye, kuma babu wani yunkurin kashe shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
